Da Ɗuminsa: EFCC ta samu umarnin kama tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello
Babbar Kotun Tarayya da ke zaman ta a Abuja ta baiwa Hukumar hana yiwa tattalin arziki ta’annati damar kama tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello a shirye-shiryen kama shi ranar Alhamis.
Mai Shari’a Emeka Nwite ne ya bada damar kama shi a ranar Laraba bayan neman da hukumar tayi na kama shi.
KARANTA WANNAN LABARIN:Kotu ta tsare mutane 5 bisa zarginsu da fashi da makami
Wannan na zuwa ne bayan Babbar Kotun Kogi ta bada umarnin hana kamawa da tsarewa ko hukunta tsohon Gwamnan.