Kotun Ilorin ta tsare ƴan ƙungiyar asiri 14
A ranar Laraba ne wata kotun Majistare ta Ilorin ta bayar da umarnin tsare wasu mutane 14 da ake zargi da hannu a kungiyar asiri ta Eiye.
Ana zargin su da hannu a rikicin kungiyar asiri da ya faru a karshen mako a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamna Bago ya bada umarnin harbin ƴan daba
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewa rundunar ‘yan sandan jihar ta kama wasu mutane 46 da ake zargi da hannu a rikicin kungiyar asiri da ya barke a birnin Ilorin a karshen mako, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum daya tare da jikkata wasu da dama.
Bayanan da ‘yan sandan suka fitar sun nuna cewa, wadanda suka shigar da karar da suka samu raunuka a fuskokinsu sakamakon harin, sun kai rahoton a ofishin ‘yan sanda cewa an kai musu farmaki ne saboda neman dalilin da ya sa aka yi cinikin N6,000 da suka yi a wurin (POS) da Ibrahim Rasheed bai samu nasara ba.
A binciken da ‘yan sandan suka gudanar, wadanda ake zargin sun far musu ne, inda suka yi awon gaba da wayoyin da kudinsu ya kai Naira miliyan 2.3, agogon hannu na Rolex daya, tsabar kudi N500,000 tare da lalata motocinsu.
Rahoton na ‘yan sandan ya ci gaba da cewa wadanda ake zargin da sauran jama’a ’yan kungiyar asiri ne na Aiye da Eiye wadanda suka kai hare-hare da raunata jama’a da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba tare da lalata dukiyoyinsu a babban birnin Ilorin da kewaye.
Alkalin kotun, Issa Agbetola, ya ki amincewa da bukatar belin wadanda ake zargin da lauyoyinsu suka gabatar kuma ya ba da umarnin a ci gaba da tsare su a gidan yari na Mandala har zuwa ranar 8 ga Mayu, 2024.
A wani labarin kuma:Da Ɗuminsa: EFCC ta samu umarnin kama tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello
Babbar Kotun Tarayya da ke zaman ta a Abuja ta baiwa Hukumar hana yiwa tattalin arziki ta’annati damar kama tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello a shirye-shiryen kama shi ranar Alhamis.
Mai Shari’a Emeka Nwite ne ya bada damar kama shi a ranar Laraba bayan neman da hukumar tayi na kama shi.