Da Ɗuminsa: FG ta ba da umarnin a gaggauta sakin tan dubu ɗari 102,000 na shinkafa da masara
Matsalar karancin abinci da ake fama da ita a kasar, haɗe da hauhawar farashin kayayyaki ya sa gwamnatin tarayya ta ba da umarnin sakin shinkafa da masara tan dubu 102,000 ga ‘yan Najeriya.
Gwamnati ta kuma bayyana cewa za ta iya shigo da duk wani gibi da za a iya samu don kara kayan masarufi.
KARANTA WANNAN LABARIN:Shugaba Tinubu ya yi ta’aziyya rasuwar Cairo Ojougboh
Mohammed Idris, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala taron kwamitin shugaban kasa kan bada agajin gaggawa na abinci, wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa, Abuja, ranar Alhamis.
Ya ce shugaban kasar ya ba da umarnin cewa “za a samar da abinci, duk abin da ake bukata.”
Matakin dai ya biyo bayan zaman tattaunawa da kwamitin ya yi, dangane da zanga-zangar da ‘yan Najeriya suka yi kan tsadar abinci da sauran kalubalen tattalin arziki.
A wani labarin kuma:NLC, TUC sun fitar da sanarwar yajin aiki a fadin kasar
Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC, da kuma kungiyar ‘yan kasuwa, TUC, sun baiwa gwamnatin tarayya sanarwar fara yajin aikin a fadin kasar, wanda zai fara cikin kwanaki 14.
Kokensu ya samo asali ne daga gazawar gwamnati wajen aiwatar da yarjejeniyar mai kunshe da abubuwa 16 tsakanin kungiyoyin kwadago (NLC da TUC) da gwamnatin tarayya a ranar 2 ga Oktoba, 2023.