Hajjin 2024: Kimanin Mutane 123 sun biya kuɗin aikin hajjin bana
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Edo sun ce akalla maniyyata aikin hajji 123 sun biya cikakken kudin aikin hajjin shekarar 2024 ma Naira miliyan 4,899.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito shugaban hukumar ta jihar Sheikh Ibrahim Oyarekhua ne ya bayyana hakan a lokacin wani taro da masu niyya da sauran masu ruwa da tsaki a aikin Hajji a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN:NLC, TUC sun fitar da sanarwar yajin aiki a fadin kasar
“Ya zuwa ranar Laraba, lokacin da muka sasanta littattafanmu bayan sanarwar kudin, daga cikin mahajjata 250, 123 sun biya cikakken kuɗin su,” in ji Oyarekhuan.
Oyarekhua ya bayyana cewa taron da maniyyata da masu ruwa da tsaki a harkar aikin Hajji ya yi ne domin sanar da fara aikin Hajji na karshe na maniyyatan jihar, wanda a yanzu an kara masa Naira miliyan 4,899 sabanin Naira miliyan 4.5 da hukumar ta sanar.
Ya kara da cewa taron ya kuma sanar da maniyyata cewa wa’adin biyan kudin aikin hajjin ya kasance ranar 12 ga watan Fabrairu yayin da duk kudaden da ake aikawa ma’aikatar aikin Hajji ta Saudiyya za su kasance ne ko kuma kafin ranar 26 ga watan Fabrairu.
“Don haka duk wanda ke da sha’awar zuwa aikin Hajji a wannan shekarar dole ne ya biya sauran kudadensa a ranar 12 ga Fabrairu ko kuma kafin ranar 12 ga Fabrairu.
“Bisa la’akari da yadda mutane ke fitowa don biyan su, muna kyautata zaton cewa jihar za ta cika gurabun 412 da hukumar NAHCON ta ba ta, saboda sauran maniyyata sun dade suna jiran a sanar da kudin tafiya na karshe don samun nasu. ,” ya kara da cewa.
Oyarekhuan, wanda ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su isar da sakon ga wadanda ba su halarci taron ba, sai dai ya umarci maniyyatan da su yi aiki da hukumar domin gudanar da aikin Hajji ba tare da wata matsala ba ta hanyar biyan cikakken adadin da kuma ba su takardun da suka dace na aikin Hajji.
A wani labarin kuma:Da Ɗuminsa: FG ta ba da umarnin a gaggauta sakin tan dubu ɗari 102,000 na shinkafa da masara
Matsalar karancin abinci da ake fama da ita a kasar, haɗe da hauhawar farashin kayayyaki ya sa gwamnatin tarayya ta ba da umarnin sakin shinkafa da masara tan dubu 102,000 ga ‘yan Najeriya.
Gwamnati ta kuma bayyana cewa za ta iya shigo da duk wani gibi da za a iya samu don kara kayan masarufi.