Gwamnatin Tarayya ta hanyar Ministar Kuɗi da Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare Zainab Ahmed ta dakatar da shirin cire Tallafin Man Fetur.
Dayake jawabi a taron daya gudana a Majalisar Dokoki a Abuja a ranar Litinin, Ministan yace an dakatar dashi har sai baba ta gani.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewa, Ƙaramin Ministan Man Fetur Timipre Sylva yace Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yace Shugaban Ƙasa baya goyon bayan cire tallafin Man Fetur.
KARANTA WANNAN LABARIN:
Wata Mata Ta Kubuta Daga Harin Wuka Da Aka Kai Mata A Jihar Imo
Sylva ya bayyana haka a lokacin da ya bayyana a shirin Newsnight na gidan Talabijin na Channels.
“Zan gaya maku a wannan lokacin cewa, cire tallafin mai gaba ɗaya bashi ne ke gaban mu ba.
“Shugaban Ƙasar Najeriya baya goyon bayan cire tallafin man fetur a wannan lokacin,” inji shi.
Ministan ya bayyana cewar daga cikin dalilan da suka sanya Gwamnatin Tarayya bata tunanin cire tallafin man fetur saboda abinda zai haifar ga ƴan Najeriya.
“Yace ” wannan abune dake buƙatar yin aiki tsakanin Gwamnatin Tarayya da Jahohi, saboda abinda ya shafi ƙasa ne. Muna aiki da Gwamnoni a halin yanzu.