Gwamnan Jahar Katsina Aminu Bello Masari a halin yanzu yana gidan Kwamishinan sa, da aka kashe a ranar Laraba.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito yadda Dr Rabe Nasir Kwamishinan Kimiyya da Fasaha aka kashe shi a gidan sa dake rukunin gidaje na Fatima Shema dake garin Katsina.
Sun dai daɓa mashi wuƙa a cikin sa, a ɗakin sa, a yayinda suka kai gawar sa zuwa cikin ban ɗaki, inda suka kulle ta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shiga Yajin Aiki: Ku gayawa Gwamnati ta cika mana buƙatun mu — ASUU ga masu ruwa da tsaki
Gwamnan tare da manyan muƙarraban Gwamnatin sa, da Jami’an tsaro a halin yanzu suna gidan Kwamishinan domin gano gawar sa.
Kwamishinan Ƴan sanda, Daraktan Kula da Ƴan Sanda Farin Kaya na Katsina, suna wurin inda suka umarci Jami’an su, dasu buɗe ƙofar wurin da aka kulle shi, bayan sun kashe Kwamishinan Dr Rabe Nasir.
Wayar Marigayin da wayar wani mutum an gansu a wurin da lamarin ya faru.
Ƴan jarida an kore su a gidan, a yayinda aka fara ƙoƙarin gano inda gawar take.
Kwamishinan Ƴan sanda daga nan sai yace an gano gawar, kuma an kaita Asibitin Ƙwararru na garin Katsina.
“An kashe shi a daren jiya, amma sai da yamma muka sani. An kama wani da ake zargi, kuma za’a cigaba da gudanar da bincike,” inji Kwamishinan Ƴan sanda.