Hukumar shirya jarrabawar kammala makarantun sikandire ta Ƙasa (NECO) ta saki sakamakon jarrabawar da daliban manyan makarantun sikandire suka rubuta a shekarar 2021.
Magatakardar hukumar Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ne ya sanar da sakin sakamakon, a shelkwatar hukumar dake Minna a jihar Neja, inda yace daga cikin dalibai 1,233,631 da suka yi rijista domin zana jarrabawar, yanzu haka dalibai 1,226,796 ne suka samu damar zama jarrabawar.
Daga cikin daliban an samu kaso 71.64 cikin ɗari (878,925) da suka samu nasarar cin Kwasa-kwasai biyar da suka haɗar da Lissafi da turanci, wanda kuma aka samu raguwa da kaso 2.25 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar 2020.
Wushishi ya kuma ce sun samu dalibai 20,003 da suka yi magudin jarrabawar wanda aka samu raguwa idan aka kwatanta da na shekarar 2020.
Ya kuma sanar da cewa sun kuma saki sakamakon jarrabawar BECE tare da umartar dalibai da su ziyarci shafin hukumar domin duba sakamakon da suka samu.