Gwamnan Jahar Enugu Ifeanyi Ugwuanyi a ranar Talata ya ɗage dokar hana zirga-zirgar ga Adaidaita, da Babur mai taya biyu, da Manyan Motoci Tipper a Al’ummomin Nkanu ta Gabas da Nkanu ta Yamma, da wasu Al’ummomi a Ƙaramar Hukumar Enugu ta Kudu.
Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi a ranar Juma’a, bayan taron gaggawa da Masu ruwa da tsaki a Ƙananan Hukumomi guda biyar a Enugu ta Gabas, ya sanya doka dake hana zirga-zirgar Adaidaita, da Babur mai Ƙafa biyu da Manyan Motoci a Yankunan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari: Dole Masu garkuwa da ƴan makaranta za su ɗanɗana Kuɗar su
Hana zirga-zirgar tuni ya haifar da yin Allah wadai daga Shuwagabannin Majami’u ciki harda Rabaran Fr Ejike Mbaka, Wanda ya bayyana sanya dokar a matsayin rashin bin Shawara.
Biyo bayan Allah wadai akan hana zirga-zirgar, Ugwuanyi ya gayyaci Shuwagabannin Ƙungiyoyin Masu Tuƙa Adaidaita, dana Babur a Jahar Enugu, da reshen Ƙungiyar Masu Manyan Motoci Tipper ta Jahar Enugu, ya zuwa taro a gidan Gwamnatin Jahar a ranar Talata.
A lokacin taron, Gwamnan ya ɗage wannan dokar, bayan zazzafan martani da aka mayar masa.
Babban Mai Taimakawa Gwamnan akan Kafafen Yaɗa Labaru Louis Amoke a cikin sanarwar daya fitar bayan taron, yace Gwamna Ugwuanyi ya ɗage dokar.
Ya bayyana cewa Shuwagabannin Ƙungiyoyin sun tabbatar da cewa ƴan ta’adda sun shiga Ƙungiyar domin ɓata masu suna, inda suka bada haƙuri akan hakan ga Gwamnan.
A cewar sa, sun sha alwashin fito da ɓata gari a cikin su, tare da goyon bayan ƙoƙarin Jami’an tsaro wajen magance ta’addanci a Jahar.