Da alamu muna cikin ruɗani a Najeriya – Bola Tinubu
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023, Bola Tinubu, a ranar Laraba ya bayyana cewa ga dukkan alamu ‘yan Najeriya sun shiga rudani game da halin da kasar ke ciki.
Tsohon gwamnan jihar Legas ya bayyana haka ne a yayin bikin cika shekaru 70 na Bishop Matthew Hassan Kukah a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: An gano gawarwaki 15 a Iftila’in Ambaliyar Ruwa na Borno – NEMA
Yayin da yake jawabi a wurin taron, Tinubu ya ce, “Na saurari ‘yan majalisar; da alama muna cikin rudani game da al’ummarmu,
“Mun gaji magana cikin harsuna daga Littafi Mai Tsarki amma bambancin mu alkawari ne na wadata.”
Dan takarar na jam’iyyar APC ya jinjina masa kan irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Nijeriya da kuma ci gaban kasar, inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai girma da aka yi masa baiwar juriya.
A wani labarin kuma: Sojojin Sama sun yi luguden wuta, sun kakkabe Mayaƙan Boko Haram 49
Akalla ‘yan ta’addar Boko Haram 49, wadanda aka fi sani da Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, sun mutu a lokacin da jirgin yakin Super Tucano guda biyu ya kai harin bam a maboyar ‘yan ta’addan guda uku a dajin Sambisa na jihar Borno.
An tattaro cewa, an kai hare-hare da dama ta sama da rundunar sojin sama, Operation Hadin Kai, a ranakun 30 da 31 ga watan Agusta, 2022, a sansanonin ‘yan ta’adda na Gargash, Minna, da Gazuwa, a karamar hukumar Bama