Kotun da ke sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta sake watsi da bukatar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP wato Atiku Abubakar da ya ce shi ne ya lashe zaben shugaban kasa da gagarumar rinjaye a zaben 23 ga watan Fabarairu.
Atiku da PDP sun cewa sun samu kuri’u fiye da na shugaban kasa, Muhammadu Buhari da APC a sakamakon da suka samu daga ‘server’ na INEC daga jami’an INEC din. Sai dai Kwamitin kotun mai dauke da membobi biyar, a ranar Larabar yau, sun yi watsi da wannan batun bisa hujjar cewa sun kasa gabatar da kwakkwaran hujja.