Maigari na Lokoja, Alhaji (Dr) Muhammad Kabir Maikarfi III, daya daga cikin manya-manyan sarakunan kasar nan da ake girmamawa ya rasu. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Kamar yadda bayanai suka fito daga fadar, Maigari wanda shi ne shugaban majalisar sarakunar gargajiya ta Lokoja ya rasu a yammacin Larabar da ta gabata yana da shekaru 80 bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sojoji Sun Farmaki Maboyan Yan bindiga, Sun Kubutar Da Mutum 3
Har ya zuwa rasuwarsa, an ce sarkin ya kasance daya daga cikin sarakunan gargajiya da suka fi dadewa a jihar Kogi, inda ya hau karagar mulki a shekarar 1992.
A cewar sanarwar a daren Larabar da ta gabata ta hannun Sakataren Majalisar sarakunan Gargajiya ta karamar hukumar Lokoja, Muhammed Nalado Usman, za a yi jana’izar marigayin ne a Lokoja ranar Alhamis da karfe 3 na rana.
A WANI LABARIN KUMA: Masu Garkuwa Sun Kashw Dan Wani Dan Majalissa A Bauchi
Wasu ‘yan bindiga sun kashe babban dan dan majalisar dokokin jihar Bauchi mai wakiltar mazabar Dass, Bala Ali, kwanaki kadan bayan sun yi garkuwa da shi.
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Burra, Ado Wakili, ya bayyana hakan a jiya a yayin zaman da mataimakin kakakin majalisar, Alhaji Danlami Ahmed Kawule ya jagoranta.