A yammacin yau Laraba ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya isa Abuja daga kasar Saudiyya, inda ya kammala ziyarar aiki ta kwanaki takwas a kasar,Punch ta rawaito.
Jirgin Buhari NAF 001 Boeing 737 ya isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da karfe 5:08 na yamma bayan ya dauki dogon zango domin kaucewa sararin samaniyar kasar Sudan sakamakon rikicin da ake ci gaba da yi tsakanin sojoji da ‘yan kungiyar Rapid Support Forces.
KARANTA WANNAN LABARIN: A Yau Ne Buhari Zai Dawo Daga Saudiyya
Ya isa Abuja ne “bayan kusan sa’o’i bakwai na tafiyar awa hudu zuwa biyar daga Jeddah zuwa Abuja saboda halin da ake ciki a Sudan wanda ke bada damar kaucewa zirga-zirgar sararin samaniyar kasar baki daya,” wata sanarwa da babban mataimaki na musamman na shugaban kasar ka Kafofin yada labarai da wayar da kan jama’a, Garba Shehu ya fitar a yammacin Laraba.
Shehu ya ce, “Jirgin da aka mayar da shi ya taso ne daga Jeddah, a Saudi Arabiya ta hanyar Eritrea, Habasha, Kenya, Uganda, DRC, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Kamaru da kuma Najeriya.”
Da isar shugaban ya samu tarba daga shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya Farfesa Ibrahim Gambari da mataimakin sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya Danmallam Mohammed da ke wakiltar sufeto-janar na ‘yan sanda da kuma babban darakta hukumar leken asiri Yusuf Bichi.
Buhari wanda ya kai ziyarar kwanaki takwas a birnin Makkah na kasar Saudiyya, ya kuma gudanar da aikin Umrah inda ya gana da takwaransa na Jamhuriyar Chadi, Mahamat Deby-Itno, inda ya yi Allah wadai da rikicin kasar Sudan, inda ya yi kira domin tsagaita wuta.
Ya kuma ziyarci Masallacin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam tare da zagaya wajen baje kolin tarihin rayuwar Manzon Allah a birnin Madina na duniya inda ya kai kara domin a samu daidaiton fahimtar addinin Musulunci ta hanyar gyara kuskuren fahimtar addinin da aka dade shekaru aru-aru.
Wannan dai ita ce ziyararsa ta karshe zuwa Masarautar a matsayin shugaban kasa.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Hukumar NSCDC Ta Gayyaci Kwamandan Adamawa
Babban kwamandan hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC), Ahmed Abubakar Audi, ya gayyaci kwamandan rundunar na jihar Adamawa, Muhammad Bello, zuwa hedikwatar hukumar ta kasa domin bayyana irin rawar da ya taka wajen adalcin kammala zabe a jihar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Kwamanda Olusola Odumosu, ya fitar a ranar Laraba, ta ce hakan na da nasaba da cece-kucen da aka samu a zaben gwamnan jihar Adamawa da aka kammala, inda ake zargin hukumar da hada baki da wasu jami’an tsaro.
Comments 1