Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Juma’a 21 ga watan Afrilu da kuma Litinin 24 ga watan Afrilu, 2023, a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan karamar Sallah na bana.
Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, a cewar wata sanarwa da babban sakatarenta, Dr Shuaib Belgore, ya fitar ranar Laraba,kamar yadda Punch ta rawaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Dawo Abuja Daga Saudiyya
Ya kuma taya daukacin al’ummar musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan.
Ogbeni Aregbesola ya yi kira ga daukacin al’ummar Musulmi da su yi koyi da kyawawan dabi’u na kyautatawa, soyayya, hakuri, zaman lafiya, kishin kai, sadaukarwa da kyautata makwabtaka, kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi misali da shi.
“Kame kai, kin kai, sadaukarwa da zurfin sanin yakamata da ke tare da lokacin azumi bai kamata ya kare ba sai dai a kiyaye shi kuma a inganta shi, domin ya zama nagartaccen mutum kuma mai bauta ta gaskiya,” Ministan ya shawarci dukkan musulmi.
Aregbesola ya ba da tabbacin cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya jajirce sosai wajen ganin an mika mulki cikin lumana bayan nasarar zabe. Ya ba da tabbacin gwamnati ta himmatu wajen samar da tsaro ga rayuka da dukiyoyin kowane dan kasa da kuma baki a kasar.
Ministan ya yabawa dukkan hukumomin tsaro bisa nasarorin da aka samu a yaki da masu aikata laifuka a fadin kasar.
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su kasance cikin tsarin tsaro na kasa ta hanyar yin taka-tsan-tsan tare da kai rahoton mutane da ayyukan da ake zargi da aikatawa ga jami’an tsaro da ke kusa da su, tare da lura da cewa tsaro alhakin kowa ne. Ya kuma shawarci ’yan Najeriya da su kai rahoton abubuwan da ake zargi da kuma mutanen da ake zargi zuwa aikace-aikacen manhajar N-Alert.
Aregbesola ya yi wa daukacin al’ummar Musulmi barka da Sallah tare da addu’ar “Amincin Allah ya tabbata a gare ku baki daya. Ameen.”
A wani labarin kuma, Gwamnatin Wata Jiha Ta Saki Sunayen Mutane 1,300 Da Za A Tantance Su A Matsayin Malamai
‘Yan takara 1,300 daga cikin sama da 11,000 da suka zana jarabawar daukar malamai a makarantun firamare na gwamnati a jihar Ekiti an tantance su domin shiga matakin karshe na daukar ma’aikata.
Shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar (SUBEB), Farfesa Femi Akinwumi wanda ya bayyana haka a Ado Ekiti yayin da ake tattaunawa da wadanda suka yi nasara, ya ce wadanda suka yi nasara da kashi 45% da sama da haka ne aka tantance su.
Comments 2