An kammala kada kuri’a a babban zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki a Abuja.
Zaben, wanda aka fara tun jiya da yammacin Laraba, ya kare da karfe 7.45 na safiyar yau a cikin tsauraran matakan tsaro da kuma sa idon wakilan masu son tsayawa takara.
Taron wanda aka shirya zai fara da karfe 3.30 na yammacin ranar Talata, ya fara sa’o’i hudu a makare da karfe 7.30 na yamma.
Sama da wakilai 2,000 daga sassa daban-daban na Jihohi da Babban Birnin Tarayya Abuja ne suka zabi wadanda suka fi so.
Masu neman tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC sun hada da: Bola Ahmed Tinubu, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, Rotimi Amaechi, Ogbonnaya Onu, Rochas Okorocha, Dave Umahi, Yahaya Bello, Tein Jack-Rich, Fasto Tunde Bakare, Emeka Nwajiuba, Ahmed Sani Yarima, Prof Ben Ayade da Ikeobasi Mokhelu.
‘Yan takara bakwai da suka karbi tikitin jam’iyyar kan Naira miliyan 100 kowanne, sun marawa tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu baya tare da hakura da takarar su.
An dakatad da zaben ne kan batutuwan da suka shafi jerin sunayen wakilai na kusan mintuna 30, inda aka ga tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya shiga zazzafar muhawara da wasu wakilai.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar dandalin Eagle Square da ke wurin taron da misalin karfe 1:20 na safiyar Laraba, kuma Kafin tafiyar sa, Buhari ya shaidawa ‘ya’yan jam’iyyar da su ci gaba da zama a dunkule, kuma su guji tada zaune tsaye.
In tunibu ne ya lashe zabe na APC to APC ta sendacewa ta Fadi zabe na 2023.