Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta FCT ta ba da rahoton bullar cutar diphtheria a cikin babban birnin tarayya Abuja.
Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta tabbatar da bullar cutar kuma tace an samu rahoton mutuwar mutum daya, kamar yadda Tribune Online ta rahoto.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Da Zai Duba Nade-Naden Da Tambuwal Ya Yi
Daraktan kula da lafiyar jama’a, Dr Saddiq Abdurrahman ne ya bayyana hakan a yau a wani taron manema labarai a Abuja.
Ya ce barkewar cutar ta sa daukar matakin gaggawa yayin da aka bude cibiyar bayar da agajin gaggawa domin tunkarar barkewar cutar.
A wani labarin kuma, ‘Yan Najeriya Suna Shan Wahala, Ina Samun Kira 30 A Kullum Na Neman Taimako – Bwala
Mataimaki ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Daniel Bwala, ya koka da yadda ake fama da wahalhalun da kasar ke fuskanta.
Bwala, wanda tsohon dan majalisar tarayya ne, ya koka da tsadar kayayyakin masarufi a kasar, da suka hada da kayan abinci, sufuri, kayayyaki da ayyuka, magunguna da kudaden makaranta.
A wani sakon da ya wallafa ta shafin Twitter da aka tabbatar a ranar Lahadi, Bwala ya yi ikirarin cewa baya samun kasa da kiraye-kiraye 30 daga mutane a kullum suna neman taimako.