Gwamnatin jihar Sokoto ta nada kwamitin mutane tara domin tabbatar da bin umarnin gwamnati na rusa nadin sarakunan gargajiya, da kuma dakatar da nade-naden mukamai da gwamnatin tsohon Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta yi, Vanguard ta rahoto.
Wakilan kwamitin su ne Alh. Muh’d Maigari Dingyadi (Katukan Sokoto) a matsayin shugaba, Alh. Muh’d Bature Shinkafi, Dr. Kulu Haruna Abubakar, Hon. Isa Sadiq Achida, Alh. Suleiman S/Fulani, Sarkin Gabas Durbawa, Barista Bello Mohammed Sokoto a matsayin mambobi.
KARANTA WANNAN: ‘Yan Najeriya Suna Shan Wahala, Ina Samun Kira 30 A Kullum Na Neman Taimako – Bwala
Sannan akwai Dr. Muhammad Umar Yabo Mamba da kuma sakataren kwamitin.
A cewar sanarwar da Sakataren Yada Labarai na Gwamna Abubakar Bawa ya fitar, ana sa ran kwamitin zai duba dukkan batutuwan da suka shafi abubuwan da aka ambata tare da kara ba Gwamnati shawara akan haka.
Haka kuma kwamitin zai magance korafe-korafen da ake yi wa sarakunan gargajiya da ake zargin sun gudanar da kansu ta hanyar da bata dace da cibiyoyin gargajiya ba.
Sannan kwamitin zai ba gwamnati shawara kan duk wani lamari da ya shafi maslahar jama’a da aka ambata a sama.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tunawa cewa gwamnan jihar bayan hawansa mulki a ranar 30 ga watan Mayu ya dakatar da dukkan Sarakunan gargajiya da tsohon Gwamnan Jihar Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya nada wanda ya ce za a sake duba su nan gaba kadan domin amfanin jama’a.
Gwamnan ya kuma soke sauya sunayen manyan makarantun jihar da duk wasu nade-naden mukamai da suka shafi Majalisunsu na mulki da sauya musu matsuguni da gwamnatin da ta shude ta sanar kwanan nan.
Ya umurci cibiyoyin da abin ya shafa da su koma sunayensu da wuraren da suke da su ba tare da bata lokaci ba.
Gwamnan a cikin sanarwar ya kuma rusa dukkanin Hukumomin Gudanarwa banda na Dokoki ba tare da bata lokaci ba.
A wani labarin kuma, Gwamnan Neja Bago Ya Rusa Hukumar Zaben Jihar
Gwamnan Neja, Hon. Mohammed Umaru Bago ya bada umarnin rusa mambobin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Neja, kamar yadda Tribune Online ta rahoto.
Wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Abubakar Usman ya fitar ta bayyana cewa gwamna Umaru Bago ya bayar da umarnin rusa hukumar zaben jihar daga ranar 29 ga watan Mayun 2023.