Gwamnatin tarayya ta sanar da ware Naira biliyan 5 ga kowace jiha ta tarayya ciki har da babban birnin tarayya Abuja, domin rage tasirin radadin cire tallafin man fetur.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a fadar gwamnatin tarayya a Abuja ranar Alhamis bayan taron majalisar tattalin arzikin kasa (NEC).
KARANTA WANNAN:Dalilin Da Ya Sa Muka Jinkirta Biyan Fansho Sama Da Watanni Bakwai – Gwamnatin Jigawa
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ya jagoranci taron na NEC ranar Alhamis.
A wani labarin kuma,Yanzu-Yanzu: APC ta zargi gwamnatin Kano da baiwa Alƙalai cin hancin miliyan 10
Jam’iyyar APC ta gargadi gwamnatin NNPP a jihar Kano da ta daina kunyatar da shugabar kotun sauraron kararrakin zabena Majalisar Dokoki ta kasa da ta Jiha, Mai shari’a Flora Azinge, sakamakon zargin cin hancin N10m da aka bada ta hannun kungiyar lauyoyin ta.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar yakin neman zaben Gawuna-Gari, Malam Muhammad Garba ya fitar ranar Alhamis.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Kano ta yi kira ga hukumomin tsaro da su zurfafa bincike a kan wannan zargi tare da gurfanar da ‘karfafan rundunonin da suka shahara wajen cin hanci da rashawa.
Jaridar PUNCH ta ruwaito yadda mai shari’a Azinge ta yi korafin cewa wasu manyan lauyoyi na yunkurin baiwa alkalai cin hanci.
Azinge ta bayyana damuwar ta cewa wannan shi ne karo na biyu da alkali ke korafi kan yadda wasu lauyoyin da ke shari’ar zabe a gabanta, suka yi kokarin lalata tsarin ta hanyar ba abokan aikinta cin hanci da rashawa.
Ta bayyana a gaban kotun a ranar Talata cewa, “kudi na yawo”, ta kara da cewa “ana rade-radin cewa ma’aikaci ya karbi Naira miliyan 10.”
Jim kadan bayan bayyana hakan, gwamnatin jihar Kano ta fitar da wani rahoto da ke cewa wasu “dakaru masu karfi da suka yi fice wajen cin hanci da rashawa suna aiki tukuru domin dakile ayyukan da jama’ar jihar Kano suka yi wa tukuru.