Yanzu-Yanzu: APC ta zargi gwamnatin Kano da baiwa Alƙalai cin hancin miliyan 10
Jam’iyyar APC ta gargadi gwamnatin NNPP a jihar Kano da ta daina kunyatar da shugabar kotun sauraron kararrakin zabena Majalisar Dokoki ta kasa da ta Jiha, Mai shari’a Flora Azinge, sakamakon zargin cin hancin N10m da aka bada ta hannun kungiyar lauyoyin ta.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar yakin neman zaben Gawuna-Gari, Malam Muhammad Garba ya fitar ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yanzu Yanzu Gwamnoni Na Taron Gaggawa Da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Kano ta yi kira ga hukumomin tsaro da su zurfafa bincike a kan wannan zargi tare da gurfanar da ‘karfafan rundunonin da suka shahara wajen cin hanci da rashawa.
Jaridar PUNCH ta ruwaito yadda mai shari’a Azinge ta yi korafin cewa wasu manyan lauyoyi na yunkurin baiwa alkalai cin hanci.
Azinge ta bayyana damuwar ta cewa wannan shi ne karo na biyu da alkali ke korafi kan yadda wasu lauyoyin da ke shari’ar zabe a gabanta, suka yi kokarin lalata tsarin ta hanyar ba abokan aikinta cin hanci da rashawa.
Ta bayyana a gaban kotun a ranar Talata cewa, “kudi na yawo”, ta kara da cewa “ana rade-radin cewa ma’aikaci ya karbi Naira miliyan 10.”
Jim kadan bayan bayyana hakan, gwamnatin jihar Kano ta fitar da wani rahoto da ke cewa wasu “dakaru masu karfi da suka yi fice wajen cin hanci da rashawa suna aiki tukuru domin dakile ayyukan da jama’ar jihar Kano suka yi wa tukuru.
Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Baba Halilu Dantiye ya sanya wa hannu, ta ci gaba da cewa, gwamnatin NNPP na kallon lamarin a matsayin jarrabawa ga gwamnati mai ci don tabbatar da an yi bincike sosai kan lamarin tare da gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.
A wani labarin kuma:Gwamnan Kano ya riƙe albashin ma’aikata da Ganduje ya ɗauka aiki
Bayan tantance al’amuran da ke faruwa a kasar nan, Sarkin Kano na 14, Sanusi Lamido Sanusi II, ya ce ‘yan Najeriya na karbar shara da yawa daga ‘yan siyasar da ke daukarsu a banza.
Ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su bari shugaban kasa, gwamnoni su tsorata su ta kowace hanya.