- Gwamnatin tarayya ta nada sabbin manyan daraktocin likitoci 11
- Babbar sakatariyar ma’aikatar lafiya ta tarayya ce ta gabatar da wasikun nadin mukamai na wa’adin shekaru hudu ga CMDs din
- An umarci sababbin CMDs da su yi aiki tare da ma’aikatan kiwon lafiya da masu ruwa da tsaki don samar da ingantacciyar yanayin aiki da nufin cimma manyan ayyuka na kiwon lafiya
Gwamnatin tarayya ta nada sabbin manyan daraktocin likitoci 11 ga gwamnatin tarayya da ta kafa cibiyoyin kiwon lafiya a kasar nan, Punch ta rawaito.
An bayyana hakan ne a ranar Alhamis, a cikin wata sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun daraktan yada labaran FMoH, Patricia Deworitshe, kuma ta mika wa wakilinmu.
KARANTA WANNAN: Za Mu Cafke duk Wasu Tsoffin Motoci Tare da Masu su – FRSC
Sanarwar ta kara da cewa, babbar sakatariyar ma’aikatar lafiya ta tarayya, Kachollom Daju ta gabatar da wasikun nadin mukamai na wa’adin farko na shekaru hudu wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Agusta, 2023, ga sabbin CMDs a Abuja.
Sabbin CMD din sune Farfesa Nyandanti Yakub Wilberforce – Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, Hong dake Jihar Adamawa; Farfesa Issa Baba Awoye – Asibitin tarayya na Neuropsychiatric, Buddo-Egba dake Jihar Kwara; Dakta Umar Faruk Abdumajid – FMC, Daura dake Jihar Katsina; Dakta Muhammad Shittu Adamu –FMC, Wase dake jihar Filato; Farfesa Shuaibu Jauro Yahya – FMC, Mubi dake Jihar Adamawa.
Sannan akwai Dakta Mercy Anugwu – FMC, Onitsha dake Jihar Anambra; Farfesa Auwalu Sani Salihu– FNPH, Dawanau dake Jihar Kano; Farfesa Rufai Ahmed – Rijistara/ Babban Jami’in Gudanarwa, Hukumar Kula da Lafiya ta Najeriya.
Sauran sun hada da Farfesa Mangwa Kortar – FMC, Makurdi dake jihar Benue; Farfesa Robinson Chukwudi Onoh – Alex Ekwueme, Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya, Abakiliki dake Jihar Ebonyi; da Dakta Nurudeen Isa – Asibitin kasa na Orthopedic, Dala dake Jihar Kano.
Daju, yace duk da haka, an umarci sababbin CMDs da su yi aiki tare da ma’aikatan kiwon lafiya da masu ruwa da tsaki a matsayin ƙungiya tare da gano duk hanyoyin da suka dace don samar da ingantacciyar yanayin aiki da abubuwan more rayuwa da nufin cimma manyan ayyuka na kiwon lafiya.
A cewarta, “Yana iya zama kalubale, amma babu wani kalubalen da ba za a iya shawo kansa ba kuma nadin da aka yi muku wata alama ce ta kwarin gwiwar da Gwamnatin Tarayya ta yi muku.”
Ta kuma bukace su da su kawo kwarewa da dimbin gogewar da suka samu tsawon shekaru domin su yi amfani da su a cibiyoyin kiwon lafiya daban-daban tare da bayyana cewa ayyukan da suke yi zai tabbatar da sabunta wa’adinsu.
Daju ta ba da tabbacin cewa ma’aikatar za ta ba da tallafin da ya dace tare da kayayyakin da ake da su don ba su damar cimma matsayin asibiti.
A martanin da ya mayar, a madadin sabbin daraktocin da aka nada, Dokta Anugwu ya bayyana godiya ga shugaban kasa Bola Tinubu da ma’aikatar da suka ga sun cancanci nadin.
“Za mu yi iya bakin kokarinmu wajen inganta rayuwar jama’armu, don tabbatar da amincewar da shugaban kasa da ma’aikatar suka yi mana, za mu sanya abin da ya kamata don ciyar da tsarin kiwon lafiya a cibiyoyinmu gaba.
“Za mu yi tafiya tare da hangen nesa na shugaban kasa kuma mu tabbatar da cewa mutanenmu sun sami mafi kyawu, ba za mu ba ku kunya ba,” inji ta.
A wani labarin kuma,Da Dumi-Dumi: FG Ta Bada Tallafin Biliyan N5bn Ga Jihohi
Gwamnatin tarayya ta sanar da ware Naira biliyan 5 ga kowace jiha ta tarayya ciki har da babban birnin tarayya Abuja, domin rage tasirin radadin cire tallafin man fetur.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a fadar gwamnatin tarayya a Abuja ranar Alhamis bayan taron majalisar tattalin arzikin kasa (NEC).