Daliban da ke karkashin kungiyar dalibai ta kasa (NANS) sun mamaye filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas domin matsawa gwamnati bukatar ganin ta warware yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da ya kwashe kusan watanni bakwai ana yi.
Ku tuna a baya NANS ta ce za ta fara zanga-zanga a filayen jiragen sama na gida da na kasa da kasa a fadin kasar daga ranar Litinin, 18 ga watan Satumba kan yajin aikin.
Ta ce matakin da ta dauka na dakile ayyukan filayen tashi da saukar jiragen sama na da nasaba da nasarorin da aka samu a zanga-zangar da ta gudanar inda aka toshe manyan hanyoyi da dama.
KARANTA KUMA: Buhari Ya Isa New York Domin Halartar Taron Majalisar Dinkin Duniya Karo Na 77
Shugaban ta NANS, wanda ya yi magana a Akure, babban birnin jihar Ondo, ya ce kafa filayen saukar jiragen saman ne don baiwa masu hannu da shuni damar raba radadin daliban da aka tsawaitawa yajin aikin.
Shugaban kungiyar NANS ta kasa Ojo Raymond Olumide, yace ‘Karshen Yajin aikin ASUU Yanzu’ daliban sun gaji da rokon bangarorin biyu su kawo karshen yajin aikin.
Olumide ya ja kunnen ASUU da kada su janye yajin aikin bayan wani karin albashi da aka yi musu amma su dage kan wasu bukatu da suka kai ga yajin aikin.
A cewarsa, “Za mu sake fara wata zanga-zanga a mako mai zuwa ta hanyar mamaye filayen jiragen sama a ranar Litinin, 19 ga Satumba, 2022 zuwa # OccupyTheAirports. Muna so mu sanar da duniya game da radadin da dalibai ke ciki.”
“Daliban Najeriya wadanda iyayensu suka kafa mulkin mallaka ba za su iya ci gaba da shan wahala a gida tare da malamanmu ba, yayin da ‘yan kalilan da suka ci gajiyar zufa da jininmu sun kai ‘ya’yansu zuwa kasashen waje.”
“Muna kira ga dalibai da su tashi mu hada kai domin mu dauki kaddarar mu a hannunmu. Bukatun mu sun kasance a bayyane kuma masu sauƙi. Muna kira ga shugabannin ASUU da su yi taro da wuri don tattaunawa kan ayyukan hadin kai da kuma tsara yadda za a tunkari mataki na gaba na gwagwarmaya.”
Ya bayyana cewa bai kamata kungiyar daliban ta sanar da ‘yan sanda ba game da zanga-zangar da aka shirya yi a filin sauka da tashin jiragen sama saboda ba a yi musu jami’an tsaro ba.
A wani labarin kuma: NULGE Kaduna Ta Yi Allah-Wadai Da Kin Amincewar Da Majalissa Tayi Na Cin Gashin Kan LGA
Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Najeriya (NULGE) reshen jihar Kaduna ta bayyana rashin jin dadin ta dangane da kin amincewa da kudirin dokar cin gashin kan kananan hukumomi da majalisar dokokin jihar Kaduna ta yi.
NULGE ta ce kin amincewa da kudirin ya zama koma baya ga ingantacciyar ci gaban jihar da ma kasa baki daya.