Mazabar Boss Mustapha sakataren gwamnatin tarayya ta dakatar da shi. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A cikin wata wasika da Majiyar Dimokuradiyya ta gani dauke da sa hannun Muazu Kabiri jami’in jam’iyyar a unguwar Gwadabawa da ke Jimeta, ya ce SGF bai bayar da gudunmawa mai ma’ana ba ga jam’iyyar a lokacin zabe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutumin da ya sha kwata don murnar nasarar Buhari a 2019 ya fice daga APC ya koma PDP
Kabiri ya koka da yadda SGF ya sha kaye a hannun jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa da na gwamna.
Ba Mustapha kadai ne fitaccen dan jam’iyyar APC da ya fadi zaben sa ba. Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyya mai mulki ta kasa, ya yi rashin nasara a rumbunsa a lokacin zaben gwamna da na shugaban kasa.
Sai dai jam’iyyar APC reshen jihar Adamawa ta yi fatali da matakin, inda ta ce mazabar ba ta da hurumin dakatar da Mustapha.
Mustapha baya cikin jerin mutane 422 na yakin neman zaben Asiwaju Bola Tinubu, zababben shugaban kasa.
A wani labarin kuma, Mutumin da ya sha kwata don murnar nasarar Buhari a 2019 ya fice daga APC ya koma PDP
Ɗan Bauchi wanda yayi wanka tare da shan ruwan kwata don murnar nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa na 2019, Aliyu Mohammed Sani, ya fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Da yake jawabi a sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) a Bauchi a ranar Larabar da ta gabata, Sani wanda aka fi sani da Ali Gayu Na Baba Buhari ya ce ya yanke shawarar ne sakamakon takaicin sa da APC ta yi watsi da shi.