A yau Litinin An samu cinkoson ababen hawa a babban Birnin Tunisiya bayan da ma’aikatan kamfanin sufurin ƙasar sun shiga yajin aikin saboda an ɗau lokaci ba a biya su albashinsu da sauran haƙƙoƙinsu ba. Kamar yadda Reuters ta ruwaito.
Mai magana da yawun kamfanin Hayat Chamtouri tace ƙungiyar ma’aikatan na zanga-zanga nuna adawa da ɗaukar lokaci ba tare da an bíyasu haƙoƙinsu ba , kana kamfanin dai na fuskantar kalubale kuɗi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yadda Mai Kokarin Samar Da Zaman Lafiya Ya Kare Da Yanke Hannu A Kano
Yajin aikin da ma’aikatan keyi ya fito da ƙalubalen ƙarancin kuɗi da kamfanonin gwamamnatin kasar ke fuskanta, a dai dai lokacin da gwamnatin shugaba Kais Saied ke fuskantar kalubalen matstalar kuɗi mafi muni.
Yajin aikin na ɓangaren sufuri ya nuna Irin ƙarfin da ƙungiyar ma’aikata ta UGTT ke dashi, wanda tayi alƙawarin ci gaba da gudanar da zanga-zanga.
Ƙungiyar da ke da mambobi kusan Miliyan 1 ta amince da yajin aikin na kwanaki biyu a sufurin sama, ƙasa da kuma ruwa , a ranakun 25 da 26 ga watan Janairu domin yin zanga-zangar akan abunda suka kira ƙoƙarin malllake kamfunan gwamamnati gida.
Yajin aikin dai zai kara matsin lamba ga gwamnatin shugaba Saied, wadda ke fuskantar adawa bayan shafe watanni 17 da kwace ikon mulkin kasar matakin da ‘yan adawar ƙasar suka bayyana a matsayin juyin mulki.
A halin da ake ciki kuma, Tunisiya na fafutukar neman rancen dalar Amurka biliyan 1.9 daga Asusun Ba da Lamuni na Duniya, domin aiwatar da wasu sauye-sauyen , ciki har da rage kashe kudade, da sake fasalin kamfanonin gwamnati da kuma rage tallafin makamashi da abinci.
A wani labarin kuma, Gwamnonin G-5 Za Su Kira wa Atiku Ruwa, Za Su Ziyarci Wani Gwamnan Arewa
A dai dai lokacin da wasu masu ruwa da tsaki ke ƙoƙarin shawo kan rikicin da ya da baibaye jam’iyar PDP Kafin zaɓen shugaban ƙasa da ke tafe a ranar 25 gawatan Febuwairun shekarar 2023, rukunin gwamnonin nan a jam’iyar ta PDP wato G-5, sun shirya zuwa Bauchi domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen gwamna Bala Muhammad karo na biyu.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa bisa samun rashin jituwa tsakanin Gwamna Bala Muhammad da wasu ‘yan siyasa na hannun daman Atiku Abubakar, Gwamnan ya yanke shawarar kulla alaƙa da Rukunin Gwammnonin G-5 domin samun sai’da.