- Kotun daukaka kara da ke garin Owerri a jihar Imo ta kori Julius Abure, sannan ta amince da Lamido Apapa a matsayin shugaban jam’iyyar LP na kasa
- Kotun ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta gaggauta tantance tare da wallafa sunayen duk wasu ‘yan takarar gwamna karkashin jagorancin Apapa daya gabatar a jihohin 3
- Kotun ta kuma yi watsi da dan takarar gwamna na jihar Imo, da wasu na bangaren LP da Abure ke jagoranta
Yanzu haka dai kotun daukaka kara da ke garin Owerri a jihar Imo a ranar Alhamis ta kori Julius Abure, sannan ta amince da Lamido Apapa a matsayin shugaban jam’iyyar Labour Party LP na kasa.
Kotun ta kuma umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta gaggauta tantance tare da wallafa sunayen duk wasu ‘yan takarar gwamna da kwamitin gadanarwa na kasa karkashin jagorancin Apapa ya gabatar a jihohin Imo, Bayelsa, da kuma Kogi.
KARANTA WANNAN: Majalisar Dokoki Ta Gargaɗi Ciyamomi Kan ‘Yan Acaba Da Ke Neman Halak
Kotun ta kuma yi watsi da takarar gwamna Sanata Athan Achonu na jihar Imo, da wasu na bangaren LP da Abure ke jagoranta.
Idan dai za’a iya tunawa a watan Afrilu ne Apapa ya ce dakatarwar da aka yi masa a matsayinsa na dan jam’iyyar ba ta da inganci, yana mai cewa ya ci gaba da zama ‘shugaban riko na halal.
A ranar 14 ga watan Agusta, jaridar PUNCH ta rawaito cewa wata kotun daukaka kara da ke zama a birnin Benin, babban birnin jihar Edo, ta tabbatar da Abure a matsayin shugaban jam’iyyar Labour na kasa.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa Obiora Ifoh ya fitar.
Kafin haka dai, a ranar 26 ga watan Mayun 2023, JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rahoto cewa wata babbar kotun jihar da ke zamanta a Edo ta yi watsi da sanarwar dakatar da Abure da wasu wakilan jam’iyyar a matakin mazabu suka yi.
Alkalin kotun, Mai shari’a Emmanuel Aihamoje, ya yi watsi da karar saboda rashin cancantar.
A wani labarin kuma, Sojoji Sun Tarwatsa Wata Matatar Man Fetur A Delta
Dakarun Operation Delta Safe sun lalata wata haramtacciyar matatar mai a yankin Ogbokoko da Atu a karamar hukumar Warri ta Kudu a jihar Delta.
Wannan ci gaban ya biyo bayan ayyukan da sojojin suka yi na yaki da satar mai a Kudu maso Kudu a ranar 23 ga Agusta 2023.