Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele ya ce sabbin takardun kudi na Naira sun tsaya cak yayin da ake ci gaba da fuskantar karancin kudin, Legit.ng ta rawaito.
Yayin da ‘yan Najeriya ke kokawa kan wahalar samun takardun kudin Naira, Emefiele wanda ya samu goyon bayan shugaban kasa da kuma AGF Abubakar Malami, ya bukaci ‘yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu, lura da cewa dukkan hannaye na kan hanya domin tabbatar da isar sabbin takardun.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaɓèn 2023: Bola Tinubu Shi Ne Mafitar ‘Yan Najeriya A Daidai Wànnan Lokaci
A wani labarin kuma, Kotun da ke Awka ta yi watsi da karar da ke neman hana CBN aiwatar da manufar sake fasalin Naira.
Babbar kotun tarayya dake Awka, ta yi watsi da karar da kungiyar Incorporated Trustees of African Initiative Against Abuse of Public Trust, ke neman dakatar da Babban Bankin Najeriya CBN da Gwamnansa Godwin Emefiele da Babban Lauyan Tarayya AGF Abubakar Malami.
Kotun dai ta yi watsi da karar da ke neman hana CBN da jami’ansu daukar duk wani mataki na tilasta aiwatar da manufar sake fasalin Naira.
Bisa ga hukuncin da kotun ta yanke a cikin Certified True Copy na odar rajista mai kwanan wata 31 ga watan Janairu, 2023 ga bangarorin, Alkalin kotun, A. Nganjiwa ya bayar da umarnin soke karar bayan la’akari da batun yanayi na shari’a da muhawarar.
Kotun ta kuma bayar da kyautar Naira 300,000 a matsayin kudin da ake tuhumar wanda ya shigar da karar ta hannun CBN da Godwin Emefiele wadanda su ne wadanda ake kara na 1 da na 2.
Yanzu haka ‘yan Najeriya na kwana a wurare daban-daban na ATM na Banki domin cirar sabbin kudi daga ATMs na banki.
A wani sabon faifan bidiyo da aka yada a Facebook, wani mutum da ya dauki bidiyon ya bayyana yadda ya ga daruruwan mutane a na’urar ATM daban-daban a kan layi da misalin karfe biyu na safe.
Rahotanni sun nuna cewa an tilastawa mutane da dama yin layi na tsawon sa’o’i biyar domin cire kudi wanda ba zai wuce N20,000 a kullum ba.
A wani labarin kuma, Labour Party Ta Musanta Labarin Wargajewarta
Jam’iyyar Labour reshen jihar Ondo ta karyata rahotannin sauya sheka da rugujewar tsarin jam’iyyar a yankin kudu maso yamma don hadewa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.
A halin da ake ciki kuma, rahotannin da kafafen yada labarai suka fitar a ranar Litinin din da ta gabata, sun yi ikirarin cewa jam’iyyar Labour a shiyyar Kudu maso Yamma ta ruguje tsarinta zuwa cikin jam’iyyar APC mai mulki gabanin babban zabe mai zuwa.