Lokacin da ya zama gwamnan Jihar Legas a shekarar 1999 Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya samu nasarar bunƙasa harajin Jihar daga Naira Miliyan 600 duk wata, zuwa Naira Biliyan 8.2 a shekarar 2007.
A daidai wannan lokacin da Nageriya ta ke cikin matsayin tattalin arziƙi, ta na buƙatar Asiwaju wanda ya ke da ƙwarewa da dabarun bunƙasa tattalin arziƙi domin samun mafita.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Tsofaffin Kudi Sun Tashi Aiki A Najeriya — CBN Ta Tabbatar
Asiwaju ya samar da tsarin kiwon lafiya kyauta ga yara ƴan shekaru 18 da kuma tsofi ƴan shekaru 65.
Ƴan Nageriya na buƙatar irin wannan tsari a daidai wannan lokaci, idan Bola ya zama shugaban ƙasa zai iya samar da shi.
Baya da wannan, Asiwaju ya kafa kwamiti na tawagar aiki wacce ta duba matsalolin lafiya a Jihar. Inda aka samar da tsarin ragewa mutane kuɗin maganin da su ke sayensa da sauki.
Bola Tinubu ya kuma samar da tsarin kula da lafiyar Ido na musamman inda aka gyarawa miliyoyin al’ummar Jihar Legas idanuwan su suke gani tangararan tare da raba musu gilashin ƙarfin gani.
Sannan ya kuma samar da tsarin magance matsalar cuta mai karya garkuwar jiki HIV/AIDS da na yaƙi da zazzaɓin cizon sauro da sauran muhimman tsare-tsare a fannin lafiya.
Shi ne ya samar da tsarin gine-gine na gidaje 500 duk shekara tare da kyautata harkokin gine-gine da gidaje gami da raya birnin Legas.
Hakan kuma ya taimaka wajen janyo hankalin masu zuba jari zuwa birnin inda harkokin kasuwanci su ka ƙara samun cigaba. Wannan tunani ya na da kyau ƴan Nageriya su ba wa Asiwaju dama ya ƙara ɗaɓɓaƙa irinsa a ƙasa gaba ɗaya domin amfanin kowa.
Sannan kuma ya samar da shirin gina gidajen malamai da na ma’aikata da na alƙalai. Masu ɗauke da abubuwan ƙawa na alfarma. Wanda hakan ya buɗe babin samar da guraben ayyukan yi kimanin guda dubu 100.
A fannin sufuri ma ya zamanantar da harkar tafiye-tafiye da zirga-zirgar ababen hawa, gami da samar da hukuma ta musamman mai kula da ɗa’a da tarbiyar al’umma masu tuƙa ababen hawa. Irin tsarin da Nageriya na buƙatar wannan tunani nasa a yau domin samar da cigaba a fannin.
Haka kuma ya samar da sabbin makarantu musamman ma Firamare da sakandire tare da sabunta waɗanda ake da su daidai da tsarin zamani gami da inganta tsarin ba da horo na musamman ga malamai da kyautata albashinsu tare da biyan kuɗin jarabawar gama sakandire WAEC da NECO kyauta.
A shekarar 1999 zuwa 2003, ya yi rukunin gine-gine guda 22 a makarantun sakandire 15 akan kuɗi Naira 130,000,00. Kana kuma a dai wannan lokaci ya sabunta rukunin ajujuwa guda 39 akan kuɗi Naira 108,689,939.
A shekarar 2003 ya samar da ƙarin sabbin makarantun sakandire guda 10. Ya gina ajujuwa guda 501 a makarantu 24 da makarantun sakandire 26. Ya sabunta wasu ajujuwa 602 a makarantun firamare 4 da makarantun sakamdire 50 tare da zuba kayan aiki da na jin daɗin ɗalibai.
Sannan ya samar da tsarin inganta tsaro da wadatacciyar wutar lantarki waɗanda su ka ƙara taimakawa wajen inganta zaman lafiya da tattalin arziƙin Jihar Legas. Duk waɗannan tsare-tsare ne waɗanda Nageriya ta ke buƙatar irinsu a yau, idan aka ba wa Asiwaju dama zai yi ƙoƙarin samar da irin wannan tsare-tsare Waɗanda har lambobin yabo ya samu a kansu.
A wani labarin kuma, Wani Sabon Bincike Ya Yi Bayani Dalla-Dalla Yadda Atiku Zai Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa
Jaridar NewsOnline ta bada rahoton cewa wani bincike da aka fitar kan zaben shugaban kasa a Najeriya a shekarar 2023 ya yi hasashen cewa dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar zai yi nasara a zaben watan Fabrairu.
Rahoton na binciken watanni tara karkashin jagorancin Dr Oludare Ogunlana na kungiyar bincike da Majalisar Tsaro ta Afirka (CASA) tare da wasu jami’an leken asiri a Amurka, Turai, da Najeriya na nuni da samun nasarar Atiku.