Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU ta kara tsawaita yajin aiki da ta fara watanni biyar da suka gabata da wasu makonni hudu.
Idan za’a tuna cewa malaman da ke yajin aikin sun rufe jami’o’in gwamnati ne a ranar 14 ga watan Fabrairu,n shekarar 2022, biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya wajen aiwatar da yarjejeniyar aiki (MoA) da bangarorin biyu suka shigar a shekarar 2020.
Shugaban kungiyar ASUU na kasa Farfesa Emmanuel Osodeke a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce an yanke shawarar kara yajin aikin ne domin baiwa Gwamnatin Tarayya damar shawo kan matsalolin da suka taso.
Wannan dai ya biyo bayan wani taron gaggawa na majalisar zartarwar kungiyar ta kasa ta gudanar a Sakatariyar kungiyar dake Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kungiyar Likitoci NMA Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Karfafa Tsaro A Birnin Tarayya
A wani labarin kuma na daban.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kara karfafa dokar hana zirga-zirgar babura a duk sassan jihar.
Hakan na zuwa ne bayan watanni hudu da gwamnatin jihar da rundunar ‘yan sandan suka dage haramcin na wani dan lokaci domin saukaka zirga-zirga a cikin watan Ramadan.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Gambo Isah, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin din nan, ya ce aiwatar da dokar ya zama dole biyo bayan barazanar da ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifukan da ke hawan babura suka yi a baya-bayan nan.
“Ana jan hankalin jama’a cewa har yanzu dokar hana zirga-zirgar babura daga karfe 22:00 zuwa 06:00 na aiki a cikin garin Katsina. Yayin da yake cikin kananan hukumomin na farko daga karfe 18:00 zuwa 06:00 na safe,” in ji kakakin ‘yan sandan.
A halin da ake ciki gwamnatin jihar Katsina ta ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu a fadin jihar domin shiga sabuwar kalandar Musulunci ta 1444 bayan hijira.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, al’adu da harkokin cikin gida Honarabul Abdulkarim Yahaya Sirika ya raba wa manema labarai a ranar Lahadin nan.
A cewar sanarwar, Gwamna Aminu Bello Masari, wanda ya bayar da umarnin gudanar da hutun, ya kuma taya daukacin al’ummar jihar murna.
Gwamnan ya kuma yi kira da a dage da addu’o’i domin samun zaman lafiya, tsaro da wadata a jihar da kasa baki daya.
Ya kuma tunatar da jama’a kan ayyana ranar Yaumul Shukhur a jihar da ta zo a ranar 1 ga watan Agusta.