l
Sanata Rabi’u Kwankwaso, Dan Takarar Shugabancin Kasa na Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, a ranar Juma’a.
Ya gana da Wike kasa da sa’o’i 24 da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, inda ya ziyarci gwamnan Rivers a Poert Harcourt.
Fatan Wike na zama mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ci tura ne a ranar 16 ga watan Yuni, lokacin da aka zabi gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin mataimakin shugaban kasan dan takarar jam’iyyar, bisa shawarar da majalisar ba da shawara ta jam’iyyar ta bayar kan zaben wanda zai tsaya matsayin mataimakin Atiku.
Majalisar ta bayar da shawarar cewa, ba Wike wanda ya zo na biyu a zaben fidda gwani na shugaban kasa a ranar 28 ga Mayu da kuri’u 237, ya dace yazama mataimakin shugaban kasa.
Majiyoyi da yawa a bangaren Wike sun ce ya kasance bai jin dadi game da yadda aka ‘aka cire sunanshi’.
.Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tun bayan da Atiku ya zabi Okowa, Wike ya rika samin zawarcin jiga-jigan jam’iyyar APC da LP.
An yi imanin hakan ya sanya gidan Wike na sirri da ke Ada George Road a Fatakwal ya zama wajan ziyaran yansiyasa da dama.