Yanzu haka dai mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bar Abuja domin wakiltar shugaba Bola Tinubu a wasu manyan tarukan kasa da kasa guda biyu a birnin Rome na kasar Italiya da kuma St Petersburg na kasar Rasha, Punch ta rawaito.
Shettima ya bar filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe na Abuja da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Lahadi zai bi sahun sauran shugabannin kasashen duniya don halartar babban taron hada-hadar hannayen jari na farko mai taken “Canza Tsarin Abinci ga Mutanen Duniya da Ci Gaba”.
KARANTA WANNAN: Cambodia: Jonathan Ya Bukaci Shugabannin Duniya Su Nemi Zaman Lafiya Ta Hanyar Dimokuradiyya
Taron dai zai gudana daga ranar Litinin 24 ga watan Yuli zuwa Laraba 26 ga watan Yuli.
“A yayin taron, mataimakin shugaban kasar zai jagoranci wani babban taro mai taken ‘Ƙirƙirar Kuɗi don Canjin Tsarin Abinci: Halin da Najeriya take ciki’ da kuma gefen taron ‘Haɓaka Haɗin gwiwar Masu ruwa da tsaki da Zuba Jari don Aiwatar da Hanyoyin Sauya Tsarin Abinci a Najeriya,’.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na fadar gwamnatin tarayya dake ofishin mataimakin shugaban kasa, Olusola Abiola ya sanya wa hannu.
Sanarwar mai taken ‘Mataimakin shugaban kasa Shettima zai wakilci shugaba Tinubu a taron tsarin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Rome na kasar Italiya da kasar Rasha da Afirka a St. Petersburg.
Ana shirya taron ne tare da hadin gwiwar Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Rome da Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya, da Asusun Raya Aikin Noma na Majalisar Dinkin Duniya, da Hukumar Samar da Abinci ta Duniya da kuma Cibiyar Kula da Tsarin Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma babban tsarin Majalisar Dinkin Duniya.
Daga nan Shettima zai zarce daga birnin Rome zuwa St. Petersburg na kasar Rasha domin wakiltar shugaban kasar a taron Rasha da Afirka da aka shirya daga ranar Laraba 26 ga watan Yuli zuwa Asabar 29 ga watan Yuli.
Yayin da yake kasar Rasha, mataimakin shugaban kasar zai bi sahun sauran shugabannin siyasa da ‘yan kasuwa a wajen taron koli na Rasha da Afirka karo na 2 da kuma dandalin tattalin arziki da jin kai na Rasha da Afirka da ke mai da hankali kan dabarun inganta dangantakar da ke tsakanin Rasha da nahiyar Afirka da dai sauransu.
Har ila yau, zai halarci tarukan kasashen biyu tare da wakilan manyan jami’an gwamnatin kasar Rasha da abin ya shafa, da kuma shugabannin ‘yan kasuwa, domin tattauna dangantakar dake tsakanin Rasha da Najeriya.
Shettima wanda ya samu rakiyar manyan jami’an gwamnati daga ma’aikatu da hukumomi, ana sa ran dawowar sa kasar nan a karshen mako.
Wannan dai ita ce ziyararsa ta farko zuwa kasashen waje tun bayan hawansa kujerar mataimakin shugaban kasa.
A wani labarin kuma,’Yan Sanda Sun Gano shanun Da Suka Bace A Kano
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta gano wasu shanu da ba a tantance adadinsu ba da ke yawo a unguwar Ranka Hotoro da ke karamar hukumar Tarauni a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya rabawa manema labarai a Kano ranar Lahadin nan.