Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar da suka yi nasara a aikin daukar ma’aikata na shekarar 2023.
Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Mataimakin shugaban kasa Shettima Ya Hilla Rome Domin Wakiltar Tinubu A Wani Taro
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rahoto cewa wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da hukumar ta fara atisayen daukar ma’aikata na shekarar 2023, wanda ya fara a ranar 12 ga watan Maris.
Babafemi ya ce wadanda suka yi nasarar samun horon za su zo ne a Kwalejin Hukumar da ke Jos da kuma Kwalejin Zaman Lafiya ta NSCDC dake Jihar Katsina.
Babafemi ya bayyana cewa dole ne ‘yan takarar su kawo rahoton horon su tare da kwafin takardun shaidarsu.
Ya kuma yi nuni da cewa, ‘yan takarar da suka yi nasara za su kawo takardun shaida na asali da kwafi, ciki har da Numbar katin shaidar zama dan kasa (NIN) da kuma fitar da takardar shaidar neman aiki ta intanet ta NDLEA.
Hukumar ta shawarci duk ‘yan takarar da suka yi nasara da su ziyarci tasharta da aka keɓe da samun cikakkun bayanan buƙatu.
DAILY POST ta tuna cewa NDLEA ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar data tantance ma’aikatantan na shekarar 2023 a watan Yuni.
A wani labarin kuma,‘Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Wasu Abokai Har Shida
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun a ranar Asabar ta tabbatar da mutuwar wasu abokanai har su shida bayan sun sha barasa a gidan abokinsu da ke Ogbogbo, karamar hukumar Ijebu ta Arewa-maso-gabas a jihar.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa ya gano cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata, a wurin shaye-shayen inda aka ce abokanan su bakwai sun taru don jin dadi.