Mataimakin shugaban kasar Gambia Badara Joof ya rasu.
Shugaba Adama Barrow, wanda ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya sanar da cewa, wannan mummunan lamari ya faru ne a kasar Indiya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Arewa Ya Umurci Jami’an Tsaro Da Su Kubutar Da Mutanen Aka Sace A Jiharsa
“Yan uwa jama’ar Gambia, cike da kaushin zuciya na ke sanar da rasuwar Mataimakin Shugaban Kasa, Mai Girma Badara Alieu Joof.”
“Lamarin mai ban tausayi ya faru ne a Indiya bayan gajeriyar rashin lafiya. Allah Ya ba shi Jannahtul Firdawsi,” ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Mataimakin shugaban kasar ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya. Shugaban bai ambaci lokacin mutuwarsa ba ko kuma bayyana ko yana jinya a Indiya.
Dangane da bayanin martabarsa akan shafin Wikipedia, Joof dalibi ne a Makarantar Sakandare ta Armitage kuma ya horar da kansa a matsayin malami a Kwalejin Malamai ta Yundum.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Joof yi digiri na farko na ilimi a Jami’ar Bristol, digiri na biyu a fannin adabin Ingilishi daga Jami’ar London, da digiri na biyu a fannin tattalin arziki daga Jami’ar Bath.
Joof ya fara aikinsa a matsayin ƙwararren malami, yana koyar da Turanci a Kwalejin Gambia.
Sannan ya kasance shugaban sashen harsuna da adabi a makarantar sakandare ta Nusrat. Ya kasance babban sakatare a ma’aikatar ilimi tsawon shekaru.
A cikin watan Maris din shekarar 2002, an ruwaito cewa an mayar da shi babban sakatare a ma’aikatar kananan hukumomi da filaye.
Joof ya yi aiki a matsayin jami’in hulda da bankin duniya a Gambia. A cikin wannan rawar, ya taimaka wa ministar ilimi mai zurfi Mariama Sarr-Ceesay wajen gabatar da sabuwar manufar ilimi ga Gambia.
A cikin shekarar 2013, Joof ya ziyarci wurare daban-daban na ayyukan a Gambiya tare da jami’an ma’aikatar noma don samun kyakkyawar fahimta game da kalubale daban-daban da suka fuskanta.
A cikin shekarar 2014, an nada Joof a matsayin Kwararren Ilimi a Dakar, Senegal zuwa Bankin Duniya.
A ranar 22 ga watan Fabrairu shekarar 2017, Shugaba Barrow ya nada Joof a matsayin Ministan Ilimi mai zurfi, Bincike, Kimiyya da Fasaha.
A wani labarin kuma, Rundunar Yan Sanda Ta Yi Karin Haske Kan Samamen da Dakaru Suka Kai Gidan Gwamnan CBN
Hedikwatar rundunar yan Sandan Najeriya a daren ranar Talata ta ce ba ta da masaniyar wani matakin na tura jami’an ‘yan sanda zuwa gidan gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele a Abuja.
Da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa ‘yan sanda na yin katsalandan a kan gwamnan CBN, jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Muyiwa Adejobi ya ce, “Ban san da wannan batu ba”.