A halin yanzu Shahararriyar kasuwar katako ta Bodija dake karamar hukumar Ibadan ta Arewa a jihar Oyo na ci da wuta,Punch ta rawaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaban APC na Kasa Adamu, Gbajabiamila Da Wasu Sun Ziyarci Tinubu
Musabbabin tashin gobarar dai har yanzu ba a iya tantancewa ba
Babbar Magana: PDP Ta Dakatar Da Shugaban Jam’iyyar da Mataimakinsa
Jam’iyyar PDP reshen jihar Legas, ta amince da dakatar da shugabanta, Philip Aivoji da mataimakinsa, Mista Tai Benedict, har sai an kammala shari’ar da kotu ta ke yi.
Shugabannin mazabar su sun dakatar da Aivoji da Benedict a ranar 14 ga watan Afrilu, bisa zarginsu da laifin keta kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar a Jihar Legas, Hakeem Amode, ya bayyana a ranar Talata a Legas cewa Kwamitin Ayyuka na Jihar ya cimma wannan matsaya ne bayan tantance sakamakon zaben 2023.
Ya bayyana cewa, a taron da kwamitin ya gudanar a ranar Talata, ya tattauna kan ceto ran babbar jam’iyyar adawa a jihar.
Ya kara da cewa, sakamakon haka kwamitin ya tabbatar da mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na Legas (shiyyar sanatan yamma), Sunday Olaifa, mukaddashin shugaban, yana jiran sakamakon shari’ar da kotu za ta yi.
Amode ya bayyana cewa kwamitin ya kuma kafa kwamitin ladabtarwa na mutum bakwai da zai binciki duk wani abu da ya shafi jami’an da aka dakatar.
“Mambobin kwamitin ladabtarwa sun hada da Cif Abayomi Kuye (Shugaba), Misis Esther Egbi (Sakatariya), Alhaji Isiaka Shodiya, Princess M.A Coker, Messrs Kayode Ariwayo, Femi Oluokun da Segun Oriyomi.
Amode ya kara da cewa ana sa ran kwamitin ladabtarwar zaben zai koma kwamitin ayyuka na jiha mako guda daga ranar da kundin tsarin mulkin ya kafa.
“Mambobin kwamitin ayyuka na Jiha a taron sun hada da Olaifa, Mista Agboola Akinpelu (shugaban matasa), Mista Ismail Olatunji (mai kula da harkokin kudi) na Jiha da Mista Adio Salami (Sakataren kungiyar na jiha) da kuma Amode.
Comments 1