Wani jarumin fim ɗan ƙasar Canada, Saint Von Colucci, ya mutu yana da shekara 22 a duniya bayan an sauya masa halittar sa har sau 12 domin yayi kama da wani mawaƙin BTS mai suna Jimin.
Colucci ya mutu ne da safiyar ranar Lahadi, 23 ga watan Afirilun 2023 a wani asibiti a ƙasar South Korea a dalilin matsalar da aka samu a tiyatar da aka yi masa ta kwanan nan. Shafin Yabaleftonline ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Shugaban APC na Kasa Adamu, Gbajabiamila Da Wasu Sun Ziyarci Tinubu
A cewar mai kula da harkokin sa, Eric Blake, Von Colucci, wanda ya koma South Korea a shekarar 2019 domin shigar harkar nishadantarwa, an ƙara yi masa tiyata ne a ranar Asabar domin a cire wasu haƙora da aka sanya masa a watan Nuwamban da ya gabata.
Bayan an yi masa aikin, sai cuta ta shiga ciki wacce ta yi sanadiyyar ajalin sa sa’o’i kaɗan bayan an gama aikin.
“Abin baƙin ciki ne kuma abin takaici.” A cewar Blake inda ya ƙara da cewa Colucxi baya son yadda kumatun sa suka koma inda tayi tunanin cewa sun cika faɗi.
Colucci ya kashe zunzurutun kuɗi har $220,000 akan aikin da aka yi masa har sau 12, waɗanda suka haɗa da daidaita fuska, gyaran hanci, gyaran gira, rage laɓɓa da sauran su.
Wata Mata Ta Tona Asirin Masu Gidan Abincin Da Suka Amfani Da Kwashe-Kwashe, Bidiyon Ya Yadu
Wata ƴar Najeriya mai amfani da sunan @talk2veee a Twitter, ta caccaki wuraren siyar da abinci masu yin ɗan gwashe, onda ta yi mamakin cewa ko hakan yana ƙara mu su yawan ribar da suke samu ne.
@talk2veee ta yi tsokacin ne a Twitter lokacin da ta banƙaɗo wani abu da ta gano lokacin da ta je kai markaɗen tumatur da tattasai.