- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya isa wurin bude matatar man Dangote.
- Matatar zata sarrafa man fetur daga nahiyar Afirka da Asiya da kuma Amurka kusan lita miliyan 38 na diesel, Kananzir da man jiragen sama kullum.
- Shugabanin kasashen Afrika akalla biyar ne ake sa ran za su halarci bude matatar man Dangote ciki har da shugaba Buhari.
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya isa wurin bude matatar man Dangote.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Matatar Mai Ta Dangote
Matatar Dangote ta na nan ne a shiyyar ciniki marar shinge da ke Ibeju-Lekki a Legas, kuma an kafa ta ne domin sarrafa man fetur daga nahiyar Afirka da Asiya da kuma Amurka kusan lita miliyan 38,na diesel, Kananzir da man jiragen sama kullum.
Sannan Najeriya zata samu rarar danyen mai da zata fitar dashi zuwa kasashen waje.
Matatar da aka kafa domin tace ganga 650,000 na danyen mai a kowace rana na canza danyen mai zuwa amfani daban-daban kamar dizal, man fetur, man jiragen sama da kananzir.
Buhari ya samu tarba daga gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da shugaban rukunin Dangote, Aliko Dangote.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, shugabanin kasashen Afrika akalla biyar ne ake sa ran za su halarci bude matatar man Dangote ciki har da shugaba Buhari.
Sauran shugabannin da ake sa ran zuwansu sun hada da shugaban Togo, Gnassingbe Eyadéma; Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo; Shugaban kasar Senegal Macky Sall; Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum; da shugaban kasar Chadi, Mahamat Deby.
A wani labarin kuma, Shugaba Buhari, Tinubu da Wasu Shugabannin Afirka 5 Sun Shirya Bude Matatar Man Dangote
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai jagoranci wasu shugabannin Afirka biyar don bude matatar mai ta Dongote mafi girma a Afirka.
Bude matatar mai ta Dangote zai fitar da Najeriya daga kasuwar shigo da mai da kawo karshen karancin mai.
Matatar mai mallakin hamshakin attajirin Afrika, Aliko Dangote, zata iya Samar da kashi 100% na abin da Najeriya ke bukata na dukkan kayan da aka tace.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, Faure Gnassingbe na Togo, Mahamat Deby na Chadi, Macky Sall na Senegal da kuma Mohamed Bazoum na Nijar za su bude matatar mai ta Dongote mafi girma a Afirka.
Har ila yau, zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai halarci bikin, kuma shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame, wanda ba zai halarta a zahiri, zai gabatar da sakon fatan alheri.