Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa wajen bikin kaddamar da faretin sojojin Najeriya 2023.
Buhari wanda ya isa dandalin Eagle Square, inda aka gudanar da faretin, da misalin karfe 10:18 na safe ya samu rakiyar shugaban ma’aikatan fadar sa Farfesa Ibrahim Gambari.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar Hisbah Tayi Ram da Wasu Kananan Yara 11 A Wurin Shakatawa
Janar din sojan mai ritaya yana sanye ne da kakin soji na bikin kuma a halin yanzu yana bita ga sama da hafsoshi 1,000 da ke shirin yin faretin.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor; babban hafsan sojin kasa, Laftanar-Gen. Faruk Yahaya, da Sufeto-Janar na ‘yan sanda Usman Baba ne suka halarci taron.
Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Oladayo Amao; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan na daga cikin manyan bakin da suka halarci taron.
A wani labarin kuma, ‘Yan Sanda Sun Fara Gudanar da Binciki Kan Kisan Wani Jigon Jam’iyyar APGA
Kwamishinan ‘yan sandan Enugu, Ahmed Ammani, ya umurci sashen binciken kisan gilla da manyan laifuka na jihar da kuma rundunar ‘yan sanda da su bankado yadda aka kashe wani shugaban jam’iyyar All Progressives Grand Alliance APGA, Mista Dons Udeh.
Kwamishinan ya bayar da umarnin a kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da gurfanar da su gaban kuliya cikin kankanin lokaci.