Gwamnatin jihar Legas ta fara rusa haramtattun gine-gine a tsibirin Banana da ke Ikoyi,Daily Post ta rawaito.
Hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas (LASBCA) da kuma sashin kula da muhalli da laifuka na musamman (Task Force) suna gudanar da aikin rusau din.
KARANTA WANNAN LABARIN:Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari Ya Isa wurin Faretin Sojoji Sanye da Kakin Soji
Babban Manajan LASBCA, Gbolahan Oki, da Shugaban Task Force CSP Shola Jejeloye ne suka jagoranci atisayen.
Kwamishinan Yada Labarai, Gbenga Omotoso, ya ce gine-ginen sun saba wa dokar ci gaban tsare-tsare na Birane da Yankin ta shekarar (2019).
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ba da umarnin rusa ginin a lokacin da ya ziyarci wurin da ginin bene mai hawa bakwai ya ruguje a tsibirin Banana.
Sanwo-Olu ya dora alhakin abin da ya faru a ranar 12 ga watan Afrilu a kan masu ci gaba da ke son samun kudi cikin gaggawa da kuma gazawar jami’an jihar.
Ya kuma zargi ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya, da hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa, NIWA, da bayar da karin wa’adin gabar tekun.
A wani labarin kuma, Hukumar Hisbah Tayi Ram da Wasu Kananan Yara 11 A Wurin Shakatawa
Jami’an hukumar Hisbah a jihar Kebbi sun kama wasu kananan yara 11 a wani wurin shakatawa da ke Birnin Kebbi babban birnin jihar Kebbi.
A cewar Daraktan Hisbah, Muhammad Sulyman, yaran sun hada da maza da mata, masu shekaru 14 zuwa 15, wadanda aka kama su da aikata laifuka daban-daban da ake zarginsu da yin illa ga rayuwarsu a matsayinsu na kanana wanda kuma abin kyama ne a addinin Musulunci.