Daga: Abbas Yakubu Yaura
Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya jagoranci manyan jiga-jigan jam’iyyarsa zuwa gidan tsohon shugaban kasa Goodluck, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.
Cikin wadanda suka ziyarci tsohon shugaban kasar akwai Sanata Kashim Shettima, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, da gwamnoni biyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nan Da Watanni Shida Ƴan Najeriya Za su Yaba Wa Mulkin APC – Buhari
Gwamnonin sun hada da Abdulrahman Abdulrazaq jihar (Kwara), Bello Matawale (Zamfara), Atiku Bagudu (Kebbi), Simon Lalong (Plateau) da Dapo Abiodun (Ogun).
Har yanzu dai ba a san ko me ya wakana a taron ba amma alamu sun nuna kan batun zaben 2023 ne.
Jam’iyyar APC ta kafa tarihi inda ta tsige Jonathan a shekarar 2015, wanda shi ne karon farko da jam’iyyar adawa ta kayar da shugaba mai ci.
A yayin zabukan shekarar 2015, jam’iyyar APC ba ta da wani abin da ta hana Jonathan da gwamnatinsa.
A wani labarin kuma Ganduje Ya Dakatar Da Rantsar Da Sabbin Kwamishinonin Biyo Bayan Rugujewar Gini, Ambaliya
Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da bikin rantsar da sabbin kwamishinonin da aka shirya gudanarwa a gobe Laraba domin karrama wadanda suka makale a wani ginin bene mai hawa uku da ya rufta a kasuwar GSM da ke kan titin Beirut a cikin birnin.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya fitar, gwamnan yayin da yake jajantawa wadanda lamarin ya rutsa da su, ya bayar da umarnin daukar tsauraran matakan ceto wadanda suka makale a cikin baraguzan ginin.