Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki Asiwaju Bola Tinubu ya lashe zabe a mazabarsa dake jihar Legas.
Ya kayar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da sauran ‘yan takara a rukunin sa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari Ya Kada Kuri’a, Yace APC ce Za Ta Lashe Daura Da Jihar Legas
Jaridar The Nation ta rawaito Tinubu ya kada kuri’a a mazabarsa 03, a akwati na 85, Alausa, Ikeja, Legas, da misalin karfe 10:20 na safe.
Jimillar wadanda aka amince da zaben su 43 ne, yayin da bangaren zaben ke da masu kada kuri’a 324.
Tsohon gwamnan Legas ya samu kuri’u 33, yayin da PDP ta samu kuri’a daya.
Jam’iyyar Labour ta samu kuri’u 8 yayin da YPP ta samu kuri’a daya.
A wani labarin kuma, Zaben Najeriya Na 2023: Na Yi Aiki Tukuru, ‘Yan Najeriya Za Su Ba Ni Lada, in ji Tinubu
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu, a ranar Asabar din nan ya ce ‘yan Najeriya za su saka masa da kwazonsa ta hanyar zabar sa a matsayin shugaban kasa na gaba.
Ya ce ya yi aiki tukuru a lokacin yakin neman zabe fiye da kowane dan takarar shugaban kasa kuma ‘yan Najeriya za su ba shi ladan kuri’u.