Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Sanatan Kaduna da tsakiya Sanata Uba Sani ya yabawa jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC da jami’an tsaro bisa yadda suka nuna kwarewa a aikinsu.
Sanata Uba Sani ya bayyana haka ne yayin zantawarsa da jaridar DIMOKURADIYYA jim kadan bayan ya kada kuri’a a mahaifarsa da ke Kaduna.
KARANTA HAKANAN Maqari Yayi Bayani Kan El-rufa’i Da Uba Sani
Ya ce na kada kuri’ata a zaben yan takarar shugaban Kasa da sanata da na yan majalisar wakilanmu na jam’iyyar APC.
Uba Sani ya ce “aikin zaben ya kasance cikin tsari da luma.
“Ina yabawa jam’iyyar hukumar zabe INEC da jami’an tsaro bisa kwarewar da suka nuna.
“Ina kuma yabawa al’ummar jihar Kaduna nagari da suka fito da yawa domin yin amfani da katinsu yadda ya kamata“.
Ya ce “Mu dore da wannan aikin yayin da muke hada hannu domin ciyar da jihar Kaduna da Najeriya gaba“.
Ga wasu hotuna a kasa ku duba
A Wani Labarin Kuma Zaben Najeriya Na 2023: Na Yi Aiki Tukuru, ‘Yan Najeriya Za Su Ba Ni Lada, in ji Tinubu
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu, a ranar Asabar din nan ya ce ‘yan Najeriya za su saka masa da kwazonsa ta hanyar zabar sa a matsayin shugaban kasa na gaba.
Ya ce ya yi aiki tukuru a lokacin yakin neman zabe fiye da kowane dan takarar shugaban kasa kuma ‘yan Najeriya za su ba shi ladan kuri’u.