Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada kakakin kungiyar dattawan Arewa (NEF), Dr Hakeem Baba-Ahmed a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin siyasa a ofishin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.
Dr Baba-Ahmed ya kasance yaya ga Datti Baba-Ahmed, abokin takarar Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023.
KARANTA WANNAN: Kusoshin PDP Sun Fice daga Jam’iyyar Don Marawa APC baya
Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafin sa na X (tsohon shafin Tuwita) a ranar Litinin.
Ya rubuta: “Lokaci ya yi da zan bayyana wa jama’a cewa na karɓi kira na zama mai ba da shawara na musamman kan (Siyasa) ga mataimakin shugaban kasa Shettima.
“Wannan ba lokaci ba ne na suka da za ku iya zama masu amfani wajen mayar da ƙasar. Ina da girma da ƙasƙantar da kai. Don Allah a yi mini addu’a da Nijeriya.”
A wani labarin kuma, An kama wani mutum da laifin sayar da hotuna da bidiyon tsiraicin wata budurwa
An kama wani mutum mai suna Chinedu Ezeudu dan asalin kauyen Ndi Ikpa Ezinato da ke karamar hukumar Awka ta Kudu a jihar Anambra da laifin sayar da hotuna da bidiyon wata mata tsirara a shafukan sada zumunta.
An dai zargi mutumin da fallasa waɗannan hotuna da bidiyon ne bayan yunkurin neman kudi daga hannunta ya ci tura.
Ana zargin mutumin ya sayar da bidiyon tsiraicin budurwar ga mutanen da suka bukaci hakan akan Naira dubu 3,000.
Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta cafke wanda ake zargin bayan itama mai hotunan ta kai rahoto ga ofishin kwamishiniyar harkokin mata da walwalar yara, Misis Ify Obinabo.