Kwanaki 17 da rugujewar ginin Ikoyi da ya hallaka mutane 45 a Legas, wani gini da ake ginawa ya sake rugujewa a jihar.
Mutane hudu ne ake fargabar sun mutu a ruftawar ginin da ya afku a Magbon da ke unguwar Badagry a jihar Legas.
Sai dai kuma an ceto wasu biyar yayin da aka ce wasu da dama sun makale.
Daraktar hukumar kashe gobara ta jihar Legas, Mrs Margret Adeseye, ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce jami’an agajin gaggawa sun kai daukin gaggawa kan lamarin.
A cewarta, jami’an hukumar kashe gobara ta Legas, shiyar yankin Badagry, sun garzaya wurin da lamarin ya faru.
Ta ce, “An samu labarin ruftawar wani bene a Sunny Filled, dake yankin Flour Mills, na rukunin gidajen Magbon, Badagry, Legas.
“Hukumar kashe gobara ta jihar Legas, shiyar Badagry, ta ceto mutane biyar da suka mutu daga ginin da ake ginawa, yayin da ake ci gaba da kokarin ceto sauran mutanen da suka makale.
“Wadanda lamarin ya rutsa da su, wadanda akasari masu aikin gine-gine ne, an ceto su da raunukan su, Kuma suna cikin kwanciyar hankali kuma an kai su asibitocin da ke kusa domin yi musu magani.
“Sai dai, an gano manyan maza hudu a sume har zuwa lokacin da rundunar ‘yan sandan Najeriya, reshen Morogbo da sauran jama’a ke yaba kokarin hukumar kashe gobara ta jihar Legas.”
Har yanzu dai sauran hukumomin bayar da agajin ba su yi magana kan sabon ruftawar Ginin ba