An kashe wani mafarauci yayin da aka yi garkuwa da mutane 30 a kauyen Zazzaga da ke karamar hukumar Munya a jihar Neja.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Monday Bala Kuryas, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, Ya ce lamarin ya faru ne da karfe 2 na dare ranar Talata, ya kara da cewa, “ tuni ‘yan sanda suna bin maharan domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba.
Sai dai sakataren karamar hukumar Munya James Jagaba ya shaidawa jaridar Daily trust ta wayar tarho cewa an yi garkuwa da mutane 68 da suka hada da mata da kananan yara.
“Sun zo da yawa a lokacin da wadanda abin ya shafa ke barci kuma suka mamaye al’umma. Sannan an kashe mutum daya, an harbe uku yayin da aka yi garkuwa da mutane 68,” inji shi.
Jaridar Dimukuradiyya ta rawaito Wata majiya daga unguwar ta ce ‘yan bindigar sun yi ta kai farmaki ne gida-gida.
“An harbe wani mafarauci ne a yayin da ake gwabzawar bindiga da masu laifin. Ba mu san inda mutanen da aka sace suke ba. Amma an baza jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sojoji da ’yan banga a cikin al’umma,” inji shi.
Jaridar Dimukuradiyya ta rawaito cewa Tabarbarewar tsaro a kasar dai ya kara dagulewa duk da tabbacin da hukumomin kasar suka sha yi. Domin a ranar Litinin din da ta gabata, sakataren gwamnatin jihar Neja ya ce al’ummomi biyar a karamar hukumar Shiroro na karkashin ikon ‘yan Boko Haram.