By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa An samu tashin hankali a Aramoko-Ekiti, karamar hukumar Ekiti ta Yamma a jihar Ekiti
A Jiya ne dai yayin da aka harbe wani dan sanda da kuma wani Marshall na musamman na hukumar kiyaye hadurra ta kasa, ranar Litinin da yamma lokacin da wasu ‘yan fashi da makami suka kai hari a wani reshe na wani tsohon bankin dake cikin al’umma.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Wannan dai shi ne karo na biyu da ake yi wa banki fashi, bayan da aka samu irin wannan harin a shekarar 2010.
Wani shaidan gani da ido ya bayyanawa manema labarai a Ado Ekiti jiya cewa yan fashi da makami da suka shiga garin ta hanyar Igede-Ado Ekiti sun isa bankin ne bayan awanni aiki sannan suka tayar bam a babbar kofar da ake zargin yana da karfin gaske don shiga cikin bankin.
Majiyar ta kara da cewa kafin ‘yan fashin dauke da bindigu su shigo bankin, sun bude wuta kan jami’in dan sandan dake gadi kofar, yayin da Special Marshall, wanda ke cikin motar sa ya kutsa cikin shingayen da ‘yan fashin suka tare domin hana su shiga cikin wannan waje sai dai kuma sun harbe shi a cikin wannan yanayi.
A cewar wanda lamarin ya faru a kan idonsa, illar ’yan ta’addan ya jefa garin cikin bala’in daya shafi gidaje da shaguna a yankin.
Bayan aikin wanda ya dauki kusan mintuna 30, ‘yan fashin sun tsere ta sabuwar hanyar Erijiyan Ikogosi da aka gina.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti, Sunday Abutu, ya tabbatar da cewa an kashe mutane biyu a harin na ‘yan fashin.
Eh “Yunkurin yin fashi ne, amma an dakile su. Hatta jami’an mu da jami’an Rapid Response Squad sun yi musu zazzafar kora tare da kwato motoci biyu da suka yi amfani dasu wajen aikin.
“Dan sandan da suka kashe yana wajen bankin ne yayin da jami’an hukumar FRSC na musamman suka harbe shi a nesa da bankin.’Yan sanda sun dauki matakin, kuma za mu tabbatar mun gano tushen wannan al’amari.
Comments 1