Wasu ‘yan sanda biyu ne suka rasa rayukansu a safiyar ranar Asabar, yayin da wasu ‘yan bindiga suka kona shalkwatar ‘yan sandan da ke Umuguma a karamar hukumar Owerri ta yamma a jihar Imo.
Harin dai ya zo ne sa’o’i kadan bayan mataimakin babban sufeton ‘yan sanda mai kula da shiyya ta 9, Umuahia Isaac Akinmoyede ya bar jihar bayan wata ziyarar aiki ta kwana daya.
Hakan kuma ya faru ne kwanaki kadan bayan an kashe masu gadi biyu wadanda ke cikin rundunar hadin gwiwa ta tsaro a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa motar sintiri hari a Okigwe.
Rahotanni sun Kuma nuna cewa,yan bindigar da isar su sun tare hanyoyin shiga da fita ta tashar, ciki har da na kusa da hedikwatar karamar hukumar.
Daga nan ne suka kaddamar da harin a tashar ta hanyar jefa wasu na’urorin lantarki a cikin gine-gine.
An kuma ruwaito cewa bayan sun kona ofishin, sun kuma far wa wasu jami’an tsoro, inda suka gudu domin tsira da rayukansu.
Wani ganau ya ce, ‘yan sandan biyu, abin takaici, sun yi taho mu gama da ruwan harsasai.
An ba da sunayensu kamar haka; Ifeanyi da Iyke.
An ce sun yi karatun digiri na farko a Jami’ar Jihar Imo dake garin Owerri.
Kakakin ‘yan sandan jihar, Micheal Abattam, bai samu amsa ba Kiran wayar da wakilin Jaridar Daily trust yayi masa ba.