By Abbas Yakubu Yaura
Masu garkuwa da mutanen sun sako mutane saba’in da biyar da aka yi garkuwa da su a unguwar ‘Yar Katsina da ke gundumar Kekun Waje a karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rawaito.
An yi garkuwa da mutanen da aka sako a wasu manyan hare-hare guda biyu da aka kai wa al’umma cikin watanni biyun da suka gabata.
A baya dai ‘yan ta’addan sun yi garkuwa da mazauna yankin su 61, sannan bayan kwanaki 36, suka kai farmaki cikin unguwar tare da yin awon gaba da wasu mutane 15.
“Sai dai ‘yan fashin sun rike wata yarinya ‘yar shekara shida mai suna Ummi, inda suka shaida wa iyayenta cewa sun dauke ta ne saboda suna son ta.
“Iyayen ba sa cikin wadanda aka sace.
“Daya daga cikin masu garkuwar ya ce bai haifi yaro ba a rayuwarsa don haka zai dauki yarinyar.
“Ta zama ‘yarsa kamar yadda ya yi alkawari zai kula da ita sosai. Yarinyar tana tare da su har yanzu.
“Mazauna garin sai da suka biya Naira miliyan hudu kafin a sako wadanda abin ya shafa.
“Wadanda aka sako sun riga sun sake haduwa da iyalansu. Wani bangare na sharuddan da masu laifin suka bayar shi ne cewa dole ne ‘yan banga su kwance damara,” in ji wani mazaunin garin Sadiq.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ba’a samu jin ta bakinsa ba har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.