Rundunar Yan sandan kasar Kenya ta harammatawa masu karatun Digiri shiga sabon tsarinta na daukar sabbin jami’an rundunar guda dubu biyar, kamar yadda Jaridar Kasar ta Daily Nation ta ruwaito.
Wani Babban jami’in rundunar dake kasar ya ce, Rundunar ta dauki wannan matakin ne domin samun dai-daito kan albashin jami’anta da suka kammala makaratun su, mai cike da ce-ce-ku-ce.
Rahotanni sun nuna cewa, Shirin daukar sabbin jami’an a kasar Kenya za’a fara shi ne a gobe Alhamis Wanda ke bukatar akalla darajar “D” zuwa sama a jarabawar kamamla makarantar Sakandare.
A halin da ake ciki dai, bincike ya nuna cewa, Kenya ta dade tana amfani da karfin tuwo wajen tabbatar da doka a tsakanin al’uma, wanda hakan yakan haifar da mace-mace, amma ba kasafai ake dorawa jami’an tsaro laifi ba.
A wani labarin Kuma na daban.
Gobara ta kama a Gadar Lagos, ta laƙume Shaguna da dama
Shaguna da dama a wajen Gadar Apgbo dake Ebute Ero ta Lagos sun ƙone ƙurmus, bayan Gobara ta tashi a Gada da sanyin safiyar ranar Laraba.
Gobarar, wanda ta fara da misalin ƙarfe 1, ta kawo cunkoso a wajen, kuma ta shafi Harkokin Kasuwanci, a yayinda Jami’ai ke ƙoƙari domin magance ta.
Ofishin Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa dake Lagos Ibrahim Farinloye yace Ma’aikatar Ayyuka ana kira data kulle hanyar, tare da gudanar da bincike, domin gano lafiyar gadar domin cigaba da amfani da’ita.
Yace “Shaguna da dama sun ƙone. Wurin da lamarin ya faru shine Ebutte Ero. Shagunan da suka ƙone yawancin su Kayayyakin Haɗa Biredi da cin cin.
NEMA ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 6:00, an kuma turo Ma’aikatan Hukumomi Kashe Gobara na Ƙasa dana Jaha. Kuma har yanzu ba’a san abunda ya haddasa Gobarar ba.”
Farinloye ya buƙaci masu Motoci dasu yi amfani da wata hanyar.
Yace “zirga-zirga daga hanyar Ikorodu, suyi amfani da Jibowu zuwa Yaba da Onyingbo, daganan zuwa Adeniji zuwa Ebutte Ero ko kuma su cigaba zuwa hanyar Marina.