An kaiwa dan takarar gwamnan jihar Ribas a Jam’iyyar Accord, Cif Dumo Lulu-Briggs hari a ranar Asabar a karamar hukumar Etche da motarsa wacce harsashi baya hudawa.
Lulu-Briggs da kansa ya tabbatar da kai harin inda ya ce an sanar da shi cewa an kai wa sakatariyar jam’iyyar Accord a Igbo dake karamar hukumar Etche hari tare da lalata ta wanda kuma ya yanke shawarar ziyartar ofishin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kaduna 2023: Sanata Uba Sani Ya Yi Alkawarin Tallafawa Mata Da Matasa Muddin Aka Zabe Shi
Ya ce a wannan lokacin ‘yan daba suka bude masa wuta tare dashi da magoya bayansa.
Ya bayyana alhininsa game da yadda al’amura ke faruwa a Rivers ya kara da cewa jihar ta koma daji.
Ya kara da cewa ya yi yunkurin kiran kwamishinan ‘yan sanda, CP Okon Effiong Okon a lokacin da abin ya faru amma layinsa bai shiga ba.
A wani labarin kuma, Daraktar Yakin Neman Zaben Dan Takarar Shugaban Kasa Tinubu, Ta Bar APC
Daraktar kungiyar farar hula ta kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a jam’iyyar APC, Najatu Muhammad, ta fice daga jam’iyyar gabanin babban zaben 2023 mai zuwa.
Ta sanar da murabus din nata ne a wata takarda mai dauke da kwanan watan 19 ga watan Junairu 2023 ta kuma aikewa Sanata Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na kasa.
Muhammed, wadda ita ce kwamishiniya ta kasa a hukumar kula da aikin ‘yan sanda (PSC), ta ce kalubalen da Najeriya ke fuskanta na bukatar ta ci gaba da fafutukar ganin an samar da kasa mai inganci da lamiri mai kyau.