A yayin da ake ci gaba da fuskantar kalubale na nau’ikan ta’addanci daban daban babu dare babu rana musamman a Arewacin Najeriya, mun samu cewa ‘yan ta’adda sun sake kai wani mummunan hari jihar Katsina. Harin da ya auku da sanyin safiyar ranar Asabar da ta gabata a kauyen Zaka na karamar hukumar Safana, ya salwantar da rayukan ‘yan uwan juna uku da suka fito daga ciki daya kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito. An gabatar da gawawwakin wadanda suka riga mu gidan gaskiya a fadar sarkin Katsina, Mai Martaba Abdulmumin Kabir, bayan an garzaya da su da Yammacin Asabar tare da Mahaifiyar su cikin zubar hawaye. Dogaran fadar Katsina sun shawarci ‘yan uwan wadanda suka riga mu gidan gaskiya da su koma da gawawwakin zuwa mahaifar su domin gudanar da jana’iza tare da shimfide su a gidan su na karshe.
Kakakin masarautar Katsina, Mallam Iro Bindawa, ya shawarci dagacin kauyen Zaka da ya bayyana wa fadar Katsina a rubuce dukkanin yadda ta kasance yayin aukuwar wannan mummunar annoba.