Gwamnan jihar Borno Farfesa Banagana Umara Zulum ya nada Bukar Tijani a matsayin sakataren gwamnatin jihar.
Zulum ya kuma sake nada Farfesa Isa Marte a matsayin shugaban ma’aikatansa.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Nollywood Tayi Babban Rashin Wata Shahararriyar Jaruma
Kakakin gwamnan Malam Isa Gusau ne ya sanar da nade-naden biyu a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta kara da cewa, Zulum ya yi la’akari da irin kwarewar da Tijjani ya samu a matsayin minista daga watan Yulin shekarar 2011 zuwa watan Satumbar 2013 da kuma mataimakin babban sakataren kungiyar (ASG/ADG) na Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Dinkin Duniya FAO.
Tijjani mai shekaru 62 a duniya haifaffen garin Damasak ne amma ya fito daga karamar hukumar Dikwa ta jihar Borno.
Tsohon ministar yana da digirin digirgir (Masters) a fannin ci gaban aikin gona na wurare masu zafi daga jami’ar karatu ta kasar Burtaniya, wacce ya kammala a shekarar 1989.
A cewar sanarwar, Farfesa Isa Marte ya fito ne daga karamar hukumar Marte ta jihar Borno kuma ya taba rike mukamin shugaban ma’aikatan gwamna Zulum a baya.
Shugaban ma’aikatan da aka sake nadawa a baya ya taba zama kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Borno daga watan Agustan shekarar 2019 zuwa Agustan shekarar 2020.
Sannan kuma ya rike kwamishinan lafiya a shekarar 2021 yayin da yake rike da mukamin shugaban ma’aikata.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Isa Marte ya rike mukamai biyu a karkashin gwamnatin Zulum.
A wani labarin kuma,Naira Biliyan 500: Tinubu Ya Rubutawa Majalisar Wakilai Wasika
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya rubutawa majalisar wakilai wasika, yana neman a yi masa gyara a kan karin kwarya-kwaryar kasafin kudin shekarar 2022 domin daukar Naira biliyan 500 domin samar da ababen more rayuwa ga ‘yan Najeriya.
Kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas ne ya karanta wasikar shugaban a zauren majalisar a ranar Larabar nan.