Dangane da yawan bidiyon da ake yi akan samun kyautar tarihi ta Duniya,Guinness World Records (GWR) ta bukaci su yan Najeriya da su taf a hakali kan lamarin
GWR ta yi wannan tsokaci ne a yayin wata tattaunawa ta Twitter da wata ‘yar Najeriyar da ta aika musu a shafinta na twitter domin sanar da su aniyar ta na kokarin gwada bajintarta
Hukumar bada kyautar Tarihi ta Duniya yayin magana da wani dan Najeriya a Twitter sun bayyana duk wani mai son kafa tarihi yana da damar hakan amma abi a hankali
KARANTA NANNaira Biliyan 500: Tinubu Ya Rubutawa Majalisar Wakilai Wasika
Wannan gargadi na zuwa ne kwanaki kadan bayan hukumar da ke bada kyautar tarihin duniya ta shawarci ‘yan Najeriya da su nemi amincewa kafin su fara kokarin karya wani tarihi
Bayan kammala kafa tarinhinta na dafa abinci na awoyi 100 a watan Mayu, da yawa sun zaburar da matasan Najeriya sun kamu da bukatar karya tarihi kamar Hilda Baci kuma suka fara yunkurin hakan
A kokarin karya ko kafa sabon tarihi, ana kyautata zaton cewa mutane da yawa sun fara raina tarihin duniya da kuma abin da yake nufi da gaske
Ba zato ba tsammani, matsayi na duniya ya zo ne lokacin da wani mai kera sket dan Kamaru, Tembu Daniel, ya kaddamar da yunkurinsa na tseren gudun fanfalaki mafi tsayi da wani mutum ya yi
Kwanan nan ‘yar kasarsa Danny Zara ta sanar da shirinta na hakura na shiga tseren gudun fanfalaki na tsawon sa’o’i 200 domin karya kundin tarihin duniya na Guinness
A WANI LABARIN KUMA
Dangote Ya Cigaba Da Zama Wanda Yafi Kowa Kudi A Afirika Shekaru 12 A Jere
Hamshakin Dan Kasuwar Najeriya Aliko Dangote Ya Cigaba da Jan zarensa a matsayin wanda yafi kowa kudi a Afirika inda ya shafe shekaru 12 a jere a wannan matsayin
Ya dara wanda ke bi masa da kudi dan Kasar Afirika Ta Kudu inda ya cigaba da rike matsayinsa na wanda yafi kowa kudi a Afirika