Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da sabunta nadin Farfesa Mojisola Adeyeye a matsayin babbar daraktar Hukumar Kula da ingamcin Abinci da Magunguna ta kasa.
Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a ranar Juma’ar nan.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa An rubuta, ” an sake nada Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye a matsayin babbar daraktar @DGatNAFDAC a karo na biyu kuma na karshe na shekaru biyar. Ta tsaya a shedkwatar hukumar da ke Abuja don ganawa da wasu Daraktoci.”
KU KARANTA KUMA Hukumar NAFDAC Ta Fadakar DaYan Najeriya Game Da Wata Na’urar Gwaji Mara Kyau
Haka kuma, wani babban ma’aikacin hukumar da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin.
Ma’aikacin ya ce an sake nada Adeyeye a matsayin shugabar hukumar NAFDAC daga ranar 1 ga watan Disambar 2022.
Adeyeye, wacce aka nada a shekarar 2017, ta zo karshen wa’adin mulkinta na farko a ranar 2 ga watan Nuwambar 2022.
Jaridar Primetimenews ta rawaito cewa, Bayan cikar wa’adin farko na Adeyeye a matsayin DG, darakta mai kula da rajistar miyagun kwayoyi da kula da harkokin hukumar ta NAFDAC, Dr. Monica Eimunjeze, ita ce ta karbi mukamin mukaddashin shugabar hukumar a ranar 12 ga watan Nuwambar 2022.
A Wani Labarin Kuma Mutane Sama Da 200 Sun Rasa Muhallansu, Yayin Da Wata Gobara Ta Tashi
Wata gobara da ta barke a al’ummar Elekahia da ke garin Fatakwal a jihar Ribas ta mayar da sama da mutane 200 marasa gidaje, yayin da kayayyaki da kadarori na miliyoyin naira suka salwanta.
Majiyoyi daga yankin sun ce gobarar da ta tashi da misalin karfe 8:30 na safe, ta tashi ne sakamakon fashewar wani abun zuba kananzir.